Wani babban jami’in gwamnatin Sudan ya bayyana cewa, babbar siyasar mafi yawancin kasashen Afirka shine goyon bayan raunana Falasdinawa da kuma nuna rashin amincewar su da siyasoshin gwamnatin Isra’ila.
Kafar yada labarai ta Iran Press shashen Afirka ta rawaito cewa an kori mataimakin daraktan harkokin Afirka a ma’aikatar kasashen wajen Isra’ila a zaman kasashen Afirka wanda aka gudanar a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia.
Lamarin ya faru ne yayin bude taron inda jami’an tsaro suka zo wajen wakilan Isra’ilan kuma suka bukaci su tashi su bar dakin taron.
Wakilan Isra’ila sun shiga dakin taron a boye ta hanyar amfanin da katin shaidar wasu saboda haka jami’an tsaro suka fitar da su.
Sedqi Kablou, wanda daya ne daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar kwaminisanci a Sudan ya bayyana cewa, abinda aka yiwa wakilan Isra’ila a taron yana nuna yadda mafi yawancin kasashen Afirka ke adawa da Isra’ila ‘yar share wuri zauna.
Adil Khalfullah, shima wanda shine mai magana da yawun jam’iyyar larabawa ‘yan gurguzu ta Sudan ya bayyanawa Iran Press cewa wasu daga cikin kasashen Afirka basa goyon bayan yarjejeniyar karni wacce wasu daga cikin shugabannin kasashe sukayi da Isra’ilan.
Sa’annan Heitam Mahmud wani babba a harkar musulunci ta Sudan ya bayyana rashin goyon bayan mutanen Sudan a wannan daidaitawar da Isra’ila kuma ya bayyana kokarin yarjejeniyar karnin da Isra’ila tayi da wasu kasashen Afirka matsayin kuskure.
Ya kuma bayyana korar wakilan Isra’ila daga zaman tarayyar Afirka ‘yar manuniya ce da take nuna Isra’ilan bata iya cimma hadafin ta a kan kasashen Afirkan ba.
Kungiyar neman ‘yancin Falasdinu kuma a nasu bangare sun bayyana godiyar su ga kasashen Afirkan bisa wannan babban kokari da sukayi.
A wani labarin na daban Falasdinawa 10 ne suka rasa rayukan su, wasun 100 kuma sukaji raunuka a wani hari da Isra’ila ta kai yankin Nablus dake Falasdinu.