Sa’o’i kalilan bayan rantsar da Kanar Assimi Goita a matsayin sabon shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali, fitaccen dan siyasar kasar Choguel Maiga ya samu mukamin Firaminista, nade-naden da ke zuwa bayan juyin mulkin ranar 24 ga watan Mayu bisa jagorancin Goita, wanda ya zama juyin mulki na biyu da kasar ta gani a watanni 9.
Kanar Goita ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasar ta Mali a karkashin gwamnatin rikon kwarya, wacce aka kafa a watan Satumban bara, wacce ta yi alkawarin yin garambawul ga kundin tsarin mulki kafin watan Oktoba da kuma gudanar da zabe a watan Fabrairun badi.
Hakan ya sanya ana fargabar rashin zaman lafiya a Mali ka iya janyo lalacewar sha’anin tsaro a yankin Sahel da ke fama da mayakan jihadi.
A makon jiya ne Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS, ta sanar da dakatar da wakilcin Mali daga cikinta, tare da kiran sojoji su mutunta yarjejeniyar da aka cimma a baya.
Yarjejeniyar na cewa, sojoji za su gudanar da gwamnatin riko na watanni18 da gudanar da zaben shugaban kasa a watan Fabrairun shekarar 2022.
Ita ma a bangarenta, kasar Faransa da kuma kasashen Yammaci sun bukaci da a dawo da mulkin kasar ta Mali kan turbar Dimokradiyya.
Wasu na zargin kasar faransa da hannu dumu-dumu a hambarar da tsohon shugaban kasar ta mali saboda ya nuna rashin amincewar sa da zaluncin yahudawan sahayoniya (Isra’ila) a kan raunanan falasdinawa.
Faransa ta shahara da haddasa fitina a kasashen duniya mabambantta musamman idan shugabanni sun saba ma muradan ta wanda hakan ke zama babbar barazana ga kasashen afirka musamman wadanda faransan tayi ma mulkin mallaka a shekarun da suka gabata.
Kungiyar kasashen yammacin afirka sun dai yi barazanar sanya ma kasar ta mali takunkumi idan ba’a samu sauyi ba amma dai ga dukkan alamu barazanar tasu batayi tasiri ba duba da cewa sojoji ‘yan juyin mulkin ga dukkan alamu suna da goyon bayan faransa.