An samu labarin cewa, za a dauko gawar Fir’auna daga kasar Masar zuwa kasar Faransa don yin bajekoli.
A cewar majiya, an dauke gawar Fir’auna ne daga kasar Faransa a shekarar 1976, inda aka mayar da ita mazauninta a Masar.
Hakazalika, za akai gawar wasu kasashe biyu don nunawa masu yawon bude ido da sha’awar kallon Fir’auna.
Faransa za ta karbi gawar Fir’auna Remses II daga kasar Masar domin yin bajekolinta ga jama’a a wani taro, RFI ta ruwaito.
Wannan na fitowa ne daga bakin mahukuntan kasar Masar, kuma shi ne karon farko da gawar za ta koma Faransa bayan shekaru 50 da barinta kasar.
A cewar mahukuntan, a ranar 7 Afrilun bana ne za a nuna gawar Fir’una a dakin aje kayayyakin tarihi da ke birnin Paris.
Hakazalika, an ce za a ci gaba da nuna gawar ne tar zuwa ranar 6 ga watan Satumban, inda za ta shafe watanni a gidan.
Manufar yin wannan hobbasa dai ba komai bane face jawo hankalin jama’a masu yawon bude ido zuwa kasar ta Faransa.
Hakazalika, ana shirya yin bajekolin ne domin nunawa duniya wannan gawa mai dogon tarihi ne ga wadanda ke fatan ganinta na tsawon lokaci.
Masani ya zubar da kwallo bayan samun labarin za a kai gawar Fir’auna Faransa Dominique Farout, wani fitacce wajen binciken kayayyakin tarihin masarautar Masar ya ce ya yi dadi da farin cikin cewa za a kai gawar Paris, France24 ta ruwaito.
A cewarsa, ya sharara hawaye bayan samun labarin za a kai gawar Fir’auna saboda an dauke gawar ne daga Faransa a 1976 bai wuce shekaru 16 ba a duniya.
Baya ga zamanta a Faransa, gawar za ta tsaya a Sydney a Australia da San Franscisco domin nunawa jama’a da sauran masu yawon bude ido a kasashen biyu.
An yi bikin nunawa duniya gawar Fir’auna
A wani labarin kuma, kunji yadda kasar Masar ta yi gangamin nunawa duniya gawarwakin Fir’aunoninsu ga ilahirin duniya.
Kasar ta yi gagarumin biki don jawo hankalin masu yawon bude ido da ziyartar kasar don ba idanunsu abinci.
Ba wannan ne karon farko da kasar Masar ke jan hankalin duniya da kayayyakin tarihi masu dimbin shekaru ba.
Source:LegitHausa