Kasar Ethiopia Ta Musanta Jita-Jitar Da Ake Yadawa Kan Madatsar Ruwan Da Take Ginawa A Kogin Nilu.
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Habasha tafara samar da wutar lantarki a madatsar ruwan da ta gina a kogin Nilu a matsayin wani muhimmin ci gaba a aikace aikance da take yi da ya lakumee makuden kudade a kasar.Fira ministan kasar Abiy Ahmad tare da rakiyar manyan jami’an gwamnati ya kai ziyarar gane ma ido cibiyar samar da wutar lantarki,
inda ya kunna Naurar dake nuna an fara aikin samar da wutar lantarki a Hukumance a kasar,
Cibiyar samar da wutar lantarki ta GERD it ace mafi girma wajen a Afrika, amma tana tsakiya a jayayyar da ake yi tsakanin kasashen Masar da kuma kasar Sudan tun bayan da aka fara aikin a shekara ta 2011,
Abey ya bayyana ci gaban da aka samu a matsayin bude wani sabon shafi a tarhin kasar
Kasar habasha ta fara wannan aiki ne domin samar da wutar lantarki da kuma samar da ci gaba ga kasa ta biyu a yawan jama’a a nahiyar Afrika, sai dai kasashen Sudan da masar suna nuna Fargabar su game da yi wuwar madatsar ruwan ta jawo musu matsala na karancin ruwan da suke amfani da shi a tekun Nilu.
Daga karshe ya musanta jita jitar da ake yadawa na cewa madatsar ruwan zata iya jawo yunwa ka gas ashen Sudan da Masar.