Jami’ar Bayero Kano za ta karrama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Dr. Akinwumi Adesina da digirin girmamawa duba da irin gudunmawar da suka bayar a fannin ilimi da ci gaban matasa.
Wata sanarwa da mai ba mataimakin shugaban majalisar dattawa shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar ce ta bayyana hakan a ranar Talata.
Sanarwar ta ce, bikin karrama wadannan mutane za a yi shi ne a ranar Asabar, 2 ga watan Maris, 2024 a yayin bukin yaye daliban jami’ar karo na 38 a sabuwar jami’ar da ke kan titin Gwarzo, Kano.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce, “Hukumar jami’ar ce ta amince da wannan kudirin na karrama su da digirin girmamawa”.
A wani labarin na daban gwamnatin Jihar Zamfara bisa jagorancin Gwamna Dauda Lawal za ta gina sabuwar Tashar Motocin Tilera guda biyu a Gusau Babban Birnin Jihar.
Dauda ya bayyana haka a wani a taro da ya gudanar a ranar Talata a gidan gwamnati da ke Gusau lokacin da yake karbar bakuncin shugabanin Kungiyar NATO da Kungiyar PTD ta masu dakon man fetur.
Lawan ya tattauna da su a kan shirinsa na gina tashar motoci a Titin Funtua zuwa Zariya da kuma Titin Gusau Zuwa Sokoto babban birnin jihar Zamfara.
Babban mataimaki na musamman kan yada labarai na gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana haka a wata takarda da yasanya wa hannu.
Da yake jawabi ga mambobin kungiyoyin biyu, Gwamna Lawal ya ce, shirin zai kai inganta hanyoyi a babban birnin jihar.
Buba nan: An Dakatar Da Wasu ‘Yan Majalisu A Zamfara
“Na ba bayar da umarnin gina wuraren Tasha Tirela a kofofin Gusau guda biyu: daya a kan titin Funtua zuwa Gusau daya kuma a kan titin Sokoto zuwa Gusau, ” Cewar Gwamna.