Gwamnan jihar Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf, ya nuna damuwarsa kan yadda ma’aikatun tsaftar muhalli da ta karota ke gudanar da ayyukansu a jihar.
BBC Hausa ta wallafa wani rahoto a shafinta inda ta ce; Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya yumarci ma’aikatun biyu su gabatar da cikakken bayanan kayayyakin aikinsu domin tabbatar da ingancinsu.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan wata ziyarar ba-zata da ya kai hukumomin, inda ya tarar da gazawar ma’aikatun tare da jami’an hukumomin.
Abba Kabir ya nuna damuwarsa kan yadda hukumomin ke gudanar da ayyukansu, duk da irin kuɗin da ya ce gwmnati na zubawa a ma’aikatun”, in ji sanarwar.
A hukumar tsaftar muhalli ta jihar, gwamnan ya tarar da motocin kwashe shara bakwai ne kawai ke aiki daga cikin 30 da hukumar ke da su, kamar yadda ya samu motocin loda wa manyan motoci (felloda) uku ne kawai ke aiki daga cikin 15 da ma’aikatar ke da su.
Sanarwar ta cea lokacin ziyarar an shaida wa gwamnan cewa ma’aikatan dindindin 10 ne kawai hukumar ke da su, yayin da sauran duka na-wucin gadi ne.
Abba Kabir ya kuma nuna damuwarsa kan halin da ma’aikatan wucin gadin suke ciki, wanda ya bayyana da zalunci ne mutum ya yi shekara 20 a matsayin ma’aikacin wucin-gadi.
Haka kuma a ma’aikatar kula da dokokin titi ta Karota, gwamna ya tarar da motoci masu yawa da suka lalace.
Inda ya buƙaci hukumar ta gaggauta kai masa cikakken rahoton motocin da ma’aikatar ke da su.
DUBA NAN: Zafi Yayi Sanadin Mutuwar Fiye Da 900 A Hajjin Bana
Abba Kabir ya ce yadda gwamnati ke zuba makudan kuɗi a hukumar tsaftar muhallin a nuna irin muradin da gwamnati ke da shi wajen tabbatar da tsaftar muhalli, to amma ya ce hukumar ta gaza yin abin da ya dace.