Manyan malaman addinin kirosta wanda ake kira da fasto sukan yi hasashen cewa wasu abubuwa zasu faru nan gaba.
Sukan bayyana cewa, wai wahayi aka musu, wasu abubuwan na faruwa, yayin da da yawa basa faruwa.
Fastoci da yawa sun yi hasashen wasu abubuwa zasu faru da shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa amma kuma cikin ikon Allah abubuwan basu faru ba.
Daga cikin abubuwan da irin wadannan fastoci suka yi kintace sun hada da.
Daily post ta ruwaito cewa, Primate Ayodele yayi kiyasin cewa, Za’a samu baraka tsakanin shugaba Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Hakanan yayi kintacen za’a kaiwa tawagar shugaban kasa, Muhammadu Buhari hari amma duka basu faru ba.
Hakanan fasto Paul Okikijesu yayi kintacen cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari da shugaban kasar Ivory coast zasu mutu amma gashi shima bai tabbata ba.
Hakanan wannan fasto yayi hasashen za’a samu rikici tsakanin Hausawa da Fulani. Ya kuma ce za’a zubar da jinin tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi, da na Sunday Igboho dana Nnamdi Kanu, da kuma na Tampolo.
Hakanan shima Fasto Johnson Sulaiman yayi kiyasin cewa Farfesa Yemi Osinbajo zai zama shugaban kasa, kuma Arewa ba zata ci zabeba a shekarar 2023.
Hakanan shima wani fasto daga kasar Ghana, Nigel Gaisie ya bayyana cewa ya hango Farfesa Yemi Osinbajo zai zama shugaban kasa a shekarar 2021.
Shima Apostle Theophilus daga jihar Ebonyi ya bayyana cewa, Farfesa Yemi Osinbajo zai zama shugaban kasa amma hakan bata faru ba.
Dama dai Sanin Gaibu sai Allah kuma duk wanda yayi ikirarin sanin Gaibu to lallai ya dauko dala ba gammo.