Wasu tsagerun matasa ɗauke da bindigu sun kashe Kansila da wani mutun daya a kauyen Koresu, karamar hukumar Odigbo jihar.
Ondo Bayanai sun nuna cewa harin wanda ake zargin matasan Ikale da kai wa ya biyo bayan harbin wata mata a a ƙauyen Kajola.
A cewa kwamandan Amotekun kuma hadimin gwamna kan tsaro, mutanen yankunan biyu sun jima ba su ga maciji.
Mutane biyu sun rasa rayukansu a ƙauyen Koresu, yankin manoma a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo lokacin da wasu ɗauke da bindigu suka kai harin ɗaukar fansa.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da Kansila mai wakiltar yankin da kuma wani Ɗan Banga da aka gano sunansa Kayode.
Har yanzun ba’a gano ainihin sunan Kansilan ba
An tattaro cewa yan bindigan sun kai harin ne ranar Asabar sakamakon harbe wata mata a kauyen Kajola, ƙaramar hukumar Okotipupa.
‘Yan bindigan waɗanda ake zargin matasan Ikale ne sun yi kaca-kaca da gonakin mutanen ƙauyen.
Wani mai suna Christiana Umukoro, ya tabbatar da harin yace mahaifinsa ya ci duka a hannun maharan.
Ya bayyana cewa kusan kashi 95 cikin 100 na mazauna ƙauyen sun tsere domin ceton rayuwarsu.
Mashawarci na musamman ga gwamna Oluwarotimi Akeredolu kan harkokin tsaro kuma kwamandan Dakarun Amotekun, Chief Adetunji Adeleye, yace tuni aka kai gawarwakin mutanen biyu ɗakin ajiyar gawa.
Wane mataki hukumomi suka ɗauka?
Adeleye, wanda ya musanta kashe dakarun Amotekun a harin, yace komai ya koma dai-dai a ƙauyen.
Yace an jigbe sojoji, yan sanda da jami’an Amotekun a ƙauyen
A cewarsa, “Akwai wata tsohuwar gaba tsakanin iyalan Oluku na Ikale a Okotipupa da manoman Oyo/Osun dake zaune a ƙaramar hukumar Odigbo.”
“Mutanen Oyo/Osun manoma hatsi ne kuma suna faɗa da juna ne kan mallakin gonaki.
Wannan sabuwar rigimar ta kunno ne bayan an harbi wata mata ‘yar Kajola.”
“Muna zargin matasan Ikale suka kai harin ɗaukar fansa kan manoman, an kashe Kansilan yankin Oyo/Osun kana an kashe Ɗan Banga ɗaya ba wai ɗan Amotekun ba.”
Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Funmilayo Odunlami, tace babu ɗan sandan da harin ya shafa kuma nan ba da jimawa ba hukumar zata fitar da bayanai.