Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa, ta fara bayar da tallafin naira dubu ashirin-ashirin N20,000 ga ‘yan mata 45,000 domin tallafa wa harkokin karatunsu tare da karfafan iyayensu domin ci gaba da tura su zuwa makaranta.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan acikin jawabinsa na ranar samun ‘yancin kan Nijeriya karo na 63 da ya gudana a dandamalin wasanni na Sani Abacha da ke birnin Kano.
Source LEADERSHIPHAUSA
Ya ce, “Domin agaza wa karatun yara mata da kuma karfafa wa iyayensu guiwa suke turasu zuwa makaranta, mun samar da wani tsarin tallafin naira N20,000 ga sama da ‘yan mata 45,000 a matsayin wani tsarin da zai ke taimaka wa harkokin karatunsu domin su cigaba da zuwa makaranta.
“Sannan, mun sake gabatar da tsarin motocin jigilar yara zuwa makaranta domin taimaka wa sufurinsu zuwa makaranta.”
Gwamnan ya kuma ce, gwamnatinsa ta na gina sabbin makarantu a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar a wani babban yunkuri da gwamnati ke yi na magance matsalar yaran da basu zuwa makaranta da suke gararanba a kan titina.
Kazalika, ya nanata aniyar tura daliban da suka kammala karatu da daraja ta daya (Fitst class) su 1,001 domin yin digirinsu na biyu a jami’o’in kasashen waje.
Sannan, ya ce, gwamnatinsa tana da muhimman tsare-tsare da shirye-shiryen da suka sanya a gaba da za su aiwatar a bangaren bunkasa harkokin koyo da koyarwa a jihar.
Source LEADERSHIPHAUSA