Kamfanonin sadarwa a Najeriya da suka hada da MTN da Airtel da Glo da kuma 9Mobile sun fara toshe hanyar shiga shafin, Twitter a yau, kwana daya bayan da gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da shafin a Najeriya.
Kamfanonin sun ce sun samu umarni daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya don toshe hanyoyin shiga shafin Twitter a kasar bayan dakatarwar na Gwamnatin Tarayya a ranar Juma’a.
‘Yan Najeriyar masu amafani da shafin sun farka a ranar Asabar da fuskantar wahala wajen samun damar shiga shafukansu na Twitter yayin da wasu ke lalubo wasu hanyoyin sadarwar masu zaman kansu.
Kamfanonin sadarwan dai suna amsa umarnin gwamnatin najeriya ne daukan matakin katsa damar shiga manhajar tuwita a fadin kasar.
Fittatu sunyi tir da matakin
Tuni fitattun ‘Yan Najeriya da shahararrun suka fara nuna bacin ransu danagane da matakin na Gwamnatin Tarayya na hana amfani da Twitter a kasar, ba tare da la’akari da kutse da shisshigin da Twitter ke wa gwamnati ba.
Amma an ga tsohon sanata shehu sani na kaduna central yana cigaba da amfanin da kafar ta tuwita wanda yasha ruwan tambayoyi, wasu na tambayar daga ina yake wallafa sakuna a kafar sadarwar ta tuwita, wasu kuma na tambayar dalilin da yasa ya karya dokar gwamnatin kasa na hana amfani da manhajar tuwita a kasar.
Aisha Buhari ta rufe Twitter
Tuni mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari ta rufe shafinta na Twitter, domin biyayye da umurnin da uban ‘ya’yan nata yayi.
“Zan rufe shafina na Twitter a yanzu. Fatan alheri ga Najeriya,” kamar yadda ta rubuta gabanin rufe shafin.
Amma tasha suka daga ‘yan najeriya musamman fitattu wadanda suka dauki matakin nata a matsayin wanda bai dace ba.
PDP
Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta bi sahun wasu fitattu da suka hada mawaka da lauyoyi wajen Allah wadai da matakin gwamnatin tarayya na katse Twitter.