Gwamnatin tarayya ta ce kamfanonin jiragen sama da ke aiki a Nijeriya za su fara biyan diyya ga fasinjojin da suka samu jinkiri da kuma soke tashin jiragen daga watan Janairun 2024.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a ranar Talata.
Keyamo ya bayyana hakan ne yayin wani zama da kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar kan harkokin sufurin jiragen sama, inda ya kare kasafin kudin 2024 na ma’aikatarsa.
Ya ce za a rika buga cikakken jerin sunayen kamfanonin jiragen sama da ke da alhakin jinkiri ko soke tashin jirage a kafafen yada labarai a matsayin wani bangare na shirin biyan diyya.
Ya ce, “Na kira hukumar da ke kula da abokin hulda game da yadda ake mu’amala da ‘yan Nijeriya.
“Na ce kowane mako, a buga jerin kamfanonin jiragen da ba sa tashi kamar yadda aka tsara, da soke tashin jirage, jinkirin jirage, sa’o’i nawa aka samu jinkirin, akwai biyan diyya da kuma daukan mataki a matsayin wani bangare na kula da wadannan jiragen. Za mu fara aiwatar da tsarin ne a watan Janairun sabuwar shekara.”
Keyamo ya ce hanya daya da za a bi wajen cimma hakan ita ce rage biyan kudaden tikitin jiragen na kamfanonin jiragen da ke da alhakin irin wannan tsaiko da soke tashinsu.
Ya ce kowane jinkiri, akwai rahoton da mai gudanarwa zai ya bayar.

Source: LEADERSHIPHAUSA