Bayan hana yan Najeriya zuwa kasarta, kamfanin jirgin kasar UAE Emirates ya daina jigilar fasinjojin Najeriya.
Manyan Jami’an Gwamnatin Najeriya sun yi Alla-wadai da haramta baiwa yan Najeriya Biza da kasar UAE tayi.
Kamfanin jirgin saman Emirates ta UAE na bin Najeriya basussukan miliyoyin daloli da ba’a biya ta ba.
Kamfanin na jirgin Emirates ta dakatad da jigilar fasinjoji zuwa Najeriya saboda rike masa kudi da gwamnatin Najeriya tayi tsawon watanni yanzu.
Emirates ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ranar Alhamis, rahoton TheCable.
A cewar jawabin, an dakatar ne tun ranar 29 ga Oktoba, 2022.
Kamfanin yace: “Emirates ta dade tana neman mafita kan biyanta sauran kudadenta da aka rike a Najeriya.
Babban bankin Najeriya CBN yace yana duba lamarinmu kuma yayi alkawarin magance matsalar cikin kankanin lokaci.”
“Amma har yanzu Emirates bai samu wadannan kudade ba. Idan kuma ba’a biya wadannan kudade ba da kuma tsari na tabbatar da cewa za’a daina rike kudin Emirates, wannan bashi zai cigaba da taruwa ne wanda sakamakon haka zai hanamu iya biyan ma’aikata da iya jigilar fasinja.”
“Yanzu Emirates bai da wani zabi illa dakatad da shiga da fitan jiragensa a Najeriya daga ranar 29 ga Oktoba 2022.”
Wannan shine karo na biyu da Emirates zai dakatad da jigilar fasinjoji Najeriya.
Karon farko shine watan Agusta lokacin yayi sakamakon rike masa kudi $85 million.
Kamfanonin jirage na kukan gwamnati ta rike musu kudin shiga $500 million.
Hana Yan Najeriya Zuwa Dubai: Gwamnatin Tarayya Ta Caccaki Kasar UAE Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana bacin ransa bisa haramtawa yan Najeriya Biza da Gwamnatin kasar UAE tayi.
Emefiele yace Najeriya babbar kasa ce na kasuwanci kuma gwamnatin Dubai ta daina yi mata barazana.
Ya bayyana haka ne yayin zaman da majalisar wakilai ta shirya don tattauna matsalar kudin kamfanonin jiragen kasashen waje $700million da aka ki biyansu, rahoton TheNation.
Emefiele yace gwamnati na kokari don ganin an biyasu kudadensu amma abinda gwamnatin Dubai ke yi bai kamata ba.
Shi kuwa Ministan Sufurin Jirgin Sama, Hadi Sirika, yace ko a jikinsa idan gwamnati UAE ta hana yan Najeriya shiga kasarta.
Source:legithausang