Kotun Shari’ar Musulunci mai zama a Kofar Nasarawa kai tsaye ta zabi yau a matsayin ranar yanke hukunci kan shari’ar Sheikh Abduljabbar.
Tun a watan Yuli na shekarar 2021, gwamnatin Kano ta gurfanar da Malamin a Kotu kan zargin maganganun ɓatanci ga Annabi SAW.
Wannan itace zama ta 30 da za’a yi tun bayan sama da shekara guda ana yi.
An tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen Anguwar Kofar Nasarawa kusa da fadar mai martaba Sarkin Kano.
12:41 Yamma Kai tsaye an dawo daga hutun rabin lokaci, Alkali ya fara rubuta hukunci Bayan hutun kimanin mintuna ashirin da aka yi, jama’a sun fara komawa cikin kotun.
Wakilin Legit ta aiko mana da rahoton cewa: “Shi kuma alkali ya shiga wani ofishi sannan ya fara rubuta hukunci.
Abinda kowa ke fada daga bakin yan jarida shine yadda shi Abduljabar din ya fada wa alkali maganganu.
Kuma ya nuna baya neman ko wanne irin sassauci daga wajen Alkali.”
12:23 Yamma An tafi hutun rabin lokaci, sai 12:45pm za’a dawo Bayan dakatar da Abduljabbar daga magana, an tafi hutun rabin lokaci.
An dage zaman sai zuwa karfe 12:45pm.
Wakilin Legit dake kotun yace: “Yanzu an daga shari’ar sai daya saura kwata za’a kotu…
Shari’a ce da za’a iya cewa tazo karshe tun da an riga an tabbatar da zarge-zargen da ake yiwa shi wanda gwamnati ta shiga kara kan zargi da kuma abubuwan da ake masa”
12:20 Yamma Kafin yanke hukunci, AbdulJabbar ya ce Alkali karya yake masa Abduljabar ya fara fadawa Alkali kotun maganganu kuma yace alkali karya yake masa.
An dakatar da Abduljabar daga maganganu. 12:14 Yamma Alkali ya tabbatar da laifi kan AbdulJabbar.
Mai shari’a Sarki Yola ya tabbatar da duk maganganun da Abduljabbar yake yi shi ya kirkira kuma ya jinginawa ma’aiki.
Mai shari’a ya tabbatar da cewa maganganun fassara haxisan manzon Allah da Abduljabbar yace kage ne ko jingina ne, karya yake kuma hasali ma shine ya jingina kalmomin ga Ma’aiki.
Mai Shari’a ya fara karanta takardun kara, kafin yanke hukunci.
Wakilin Nigeria21 ya tabbatar mana cewa wannan shari’a tana tattare da sarkakiya sakamakon wadansu wahabiyawa da suke da matsala da Malam Abduljabbar sun shirya munafurci dangane da shari’ar.
Karashen rahoton shari’ar na zuwa…