Wani Matashi da aka gurfanar a gaban kuliya a jihar Kaduna kan laifin kan satar ledar Burodi daya.
Kotun a jihar Kaduna ta bada umurnin jefashi Kurkuku kuma saida ya kwashe wata daya da rabi a garkame.
An zargi barawon burodin da kokarin kashe sace mai burodi kum aya ji masa rauni.
Baya ga Satar Burodin, an tuhumcesa da laifin dabawa mai sayar da da Burodin, Isah Hamza, wuka.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Abubakar da farko ya musanta tuhumar da ake masa kuma aka bashi beli. Alkalin ya bada sharadin cewa ya samu wani ya tsaya masa kafin a sake shi.
Bayan kwashe kwanaki 45 a gidan yari, Abubakar ya sauya jawabinsa inda ya amince da cewa lallai ya aikata laifin.
An Gurfanar Da Wani Bawan Allah.
Lauyan mai kara, Sifeto Ibrahim Shuaibu yace: “Mai Burodin ya kashe N56,000 don jinyar raunin da yaji masa. Muna bukatar kotu ta tilastashi biyan kudin.”
Amma Alkalin, Malam Rilwanu Kyaudai, ya saki mai laifin bisa azabar kwanakin da ya kwahse a garkame kuma ya umurcesa ya biya N5,000 kudin jinyar mai burodin, rahoton Vanguard.
A wani labarin kuwa, kotun shariar da ke Rigasa, jihar Kaduna, ta bada umurnin haramta soyayya tsakanin Salisu Salele da Bilkisu Lawal saboda iyayensu ba su amince da soyayyar ba.
Alkalin, Malam Salisu Abubakar-Tureta, ya bada umurin bayan masoyan sun yarda su katse soyayyar nasu a gaban masu kula da su da jagororin unguwa, Nigerian Tribune ta rahoto.
Ya bada umurnin cewa: “Daga yau, Salisu ba zai rika haduwa ko kiran Bilkisu ba.
An haramta masa bi ta layinsu ko tsayawa kusa da gidansu Bilkisu. “Idan aka gano yana kiranta ko haduwa da ita, za a masa hukuncin da ya dace.”
A Arewacin Najeriya, doka ta amince ayi amfani da Shari’ar Musulunci wajen hukunci kan wasu laifuka.
Jihohin Arewa irinsu Kaduna, Kano, Zamfara, Neja dss na kotunan shari’a da dama.
Source:legithausang