A kaduna mai Shari’a Salisu Abubakar Tureta ya yi alkawarin zai biya wa wani saurayi Salisu Salele sadaki har N100,000 don ya auri sahibar sa
Rayila Lawal, mahaifiyar Bilkisu Lawal ne ta yi karar Salele a kotun dake kaduna kan cewa ya fito a daura aure ko kuma ya kyale mata yarta kada ya lalata mata tarbiya.
A bangarensa, Salele ya fada wa kotu cewa ba shi da sadakin aure sannan har yanzu shi dalibin jami’a ne kuma a gidan iyayensa ya ke zaune.
Wata alkalin kotun shari’a a Kaduna, malam Salisu Ababakar-Tureta, a ranar Laraba ya amince zai bada tallafin N100,000 don biya wa wani Salisu Salele sadaki ya auri sahibarsa Bilkisu Lawal.
Ya fada wa Salele ya tafi ya yi tunani kan tayin da ya masa sannan ya dawo ya fada wa kotu abin da ya yanke a ranar 6 ga watan Satumba da za a cigaba da shari’a, rahoton Vanguard.
Mahaifiyar Bilkisu, Rayila Lawal, ta kai Salele kara kotu tana neman a tilasta shi ya auri yarta idan ta gaske yana sonta ko kuma ya kyalle ta idan bai shirya yin aure ba. Rayila ta ce: “A unguwa daya muke zaune kuma yana zuwa ya ga ya ta ba tare da izinin mu ba a matsayin iyayenta.
“Na hadu da mahaifiyarsa don sanar abin da ke faruwa kuma ta ce dan ta bai shirya yin aure ba.
“Salele ya canja dabara ya dena zuwa ganin ya ta amma ya cigaba da kiranta a waya domin su hadu a wasu wurare.
“Bana son ya lalata mana tarbiyyar da muka bawa yar mu na tsawon shekaru, don haka yasa na tafi kotu na yi kararsa.”
Ta jadada cewa a shirye take ta bada auren yarta idan Salele ya shirya.
A bangarensa, Salele ya fada wa kotu cewa yana kaunar yarinayar amma bai shirya yin aure ba sai nan da shekaru biyu.
Salele ya shaida wa kotu cewa: “Har yanzu ni dalibi ne a daya cikin jami’un gwamnatin tarayya kuma ba zan so aure ya dauke min hankali ba”
“Hasali ma, ba ni da sadaki kuma har yanzu a gidan iyaye na nake zama.”
A wani rahoton, kotun shari’a a Kaduna ta umurci wata mata mai neman saki, Halima Ahmad ta mayar da katifa ga mijinta da suka kwance alaka, Suleiman Atiku.
Mr Atiku, ma’aikacin hukumar gyaran hali, tunda farko ya bukaci a dawo masa da katifansa, kafin ya amince da bukatar sakinta, The Cable ta rawaito.
Halima, wacce ke zaune a Badarawa, Kaduna, a watan Afrilun 2022, ta garzaya kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari, Jihar Kaduna ta nemi a raba ta da mijinta.
Source: LEGITHAUSA