Ƙasurgumin ɗan bindigar nan da ya addabi jihohin Sakkwato da Zamfara da kuma Katsina, Kachalla Damina, ya baƙunci lahira tare da wasu daga cikin manyan yaransa.
Wannan na zuwa ne biyo bayan artabun da sojojin Nijeriya suka yi da Kacalla tare da yaransa bayan samun wasu bayanan sirri.
Bayan samun bayanan ne rundunar sojin saman Nijeriya suka yi dirar mikiya a kan maharan yayin da suke yunƙurin zuwa ƙauyen Ƙwana da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu ta Jihar Zamfara a ranar Lahadi.
Dama ƙasurgumin ɗan bindigar na fama da munanan raunukan da ya samu yayin wata arangama da ya yi da rundunar Operation Hadarin Daji a yankin Ɗansadau, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikin yaransa.
Bayanan sirri sun bayyana wa Zagazola Makama cewa kimanin babura 58 ne ɗauke da ‘yan ta’addar yayin da suke yunƙurin kai hari suka sha luguden wuta, wanda ake kyautata zaton cewa waɗanda suka tsira ba za su wuce 11 ba.
A harin dai an hallaka sama da ‘yan ta’adda 50 tare da kuma ƙone baburansu, a yayin artabun da suka yi da sojin Nijeriya.
Kachalla Damina ya shahara wajen kashe mutanen da yin garkuwa da mutane da nufin neman kuɗin fansa daga iyalansu.
A wani labarin na daban yanayi na matsanancin zafi ya tilasta wa mahukuntan Sudan ta Kudu rufe makarantu a fadin kasar don kaucewa hatsarin da ke tattare da yanayin, duba da yadda ya ke ci gaba da ta’azzara.
Rahotanni sun ce masana yanayi sun tabbatar da cewa nan da makonni masu zuwa kasar za ta tsinci kanta cikin tsananin zafin da ba ta taba ganin irin sa a tarihi ba.
Ma’aikatar ilimi da ta lafiya sun yi hadin gwiwa wajen shawartar iyaye da su yawaita zuba wa yaransu ruwa a jiki tare da killace su a gida ba tare da barin su shiga rana ba.
Gwamnatin kasar ta yi barazanar karbe lasisin duk makarantar da aka samu a bude lokacin wannan tsananin zafi, sai dai kuma ba ta yi karin haske kan lokacin da za a bude makarantun ba.
DUBA NAN: Tashin Kayan Masarufi A Najeriya
Masana yanayi sun alakantan tsananin zafin da karancin ruwan sama, sauyin yanayi da kuma fari da kasar ke fama da shi.