Ka fita daga harkar Gwamna Umahi – APC ta gayawa Gwamna Wike.
Jam’iyyar APC a jihar Ebonyi ta caccaki gwamnan Ribas, Nyesom Wike kan yadda ya fusata kan batun sauya sheka da Gwamna David Umahi ya yi.
A ranar Lahadi jam’iyyar APC ta bayyana kalaman Gwamnan Ribas a matsayin rikon sakainar kashi da cin fuska ga bangaren shari’a.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Ebonyi, Stanley Okoro-emegha ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
READ MORE : An Ji Karar Jiniyar Gargadi Na Tashi A Kiev Babban Birnin Kasar Ukrain A Yau Asabar.
Shugaban jam’iyyar APC ya shawarci Wike da ya kyale Umahi ya kuma maida hankali wajen magance dimbin matsalolin da ke addabar jihar sa.