Jirgin yaƙin NAF ya sake komawa a karo na biyu cikin awanni 48 ya kai samame mafakar kasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji.
Rahoto ya nuna cewa da safiyar yau Litinin da misalin ƙarfe 9:00 na safe, Jirgin ya saki aƙalla bama-bamai biyu a sansanin.
Haka nan wani mazaunin Shinkafi a Zamfara yace yan bindiga sun tare matafiya a hanyar Sakkwato zuwa Gusau.
Jirgin yaƙin rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ya kai sabon hari sansanin ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji, a jihar Zamfara.
Daily Trust ta ruwaito cewa ƙasurgumin ɗan ta’addan ya tsallake rijiya da baya a wani harin ruwan bama-bamai da sojoji suka kaddamar a gidansa ranar Asabar.
Wata majiya ta shaida mana cewa Jirgin ya sake koma wa wurin da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar yau Litinin, ya saki aƙalla bama-bamai guda biyu.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a kwanakin baya, gwamnatin Zamfara ta yi ikirarin cewa Bello Turji, ya rungumi shirin zaman lafiya da gwamnatin Matawalle ta zo da shi.
A halin yanzun, wasu yan bindigan daji da ake kyautata zaton mayaƙan Bello Turji ne sun kai hari kan matafiya a babban titin Sakkwato zuwa Gusau, a ƙaramar hukumar Shinkafi.
Wani mazaunin garin Shinkafi, Murtala Wadatau, yace yan ta’addan sun toshe hanya a Kwanar Badarawa da Birnin Yero da safiyar Litinin ɗin nan.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnati ta yi ikirarin cewa ta samu galaba kan taɓarɓarewar tsaron da aka sha fama da shi a sassan Najeriya.
Gwamnatin ta bakin ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, tace duk da akwai sauran yaƙi, amma sojoji sun samu nasarori da dama kan ‘yan ta’adda.
A wani labarin kuma kun ji cewa An Kama Sojan Bogi da Wani Ƙasurgumin Dan Bindiga, Umar Namaro, a Jihar Zamfara Rundunar yan sanda ta kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga da hatsabiban infoma a ƙoƙarinta na kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar dake arewa maso yammacin Najeriya.
Dakarun sun kama Sojan bogi, da wasu masu da ake zargi da kaiwa yan bindiga Bindigu, Alburusai, Babura, kayan abinci da Kakin sojoji.
Source:legithausang