Jiragen yakin rundunar sojin sama sun ci gaba da matsa kaimi wurin kai hare-haren bama-bamai kan yan ta’adda a Kaduna.
Gwamnatin Kaduna da hukumomin tsaro a ‘yan kwanakin nan sun yi ikirarin hallaka yan bindiga da dama.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan yace nan gaba zasu sake fitar da sanarwa.
Luguden wutan jiragen rundunar sojin sama ta Najeriya kan mafakar ‘yan bindiga a yankunan kananan hukumomin Chikun, Igabi da Birnin Gwari ya yi sanadin sheke dandazon ‘yan ta’adda a Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Laraba, 7 ga watan Disamba, 2022.
Sai dai kwamishinan bai fayyace ainihin lokacin da rundunar sojin ta kai waɗan nan samame ba.
Sojoji sun kassara ‘yan ta’adda, sun ragargajiya maboyar ‘yan bindigaa dazukan wata jiha Aruwan ya ce: “Hukumar sojin sama ta ƙara matsa ƙaimi wajen ragargazar sansanonin yan fashin daji da mafakarsu da aka gano a yankunan jihar Kaduna.”
“Bayanan da gwamnatin jiha ta samu an gano tare da ragargaza wani sansani a Riyawa, Igabi LG.
Haka zalika an gano maɓoyar yan biniga a yankin Tofa, karamar hukumar Birnkn Gwari, an tashe su aiki.”
“Sojin sama sun kuma agazawa abokan aikinsu Sojojin ƙasa wajen kai samame yankunan Maidaro, Dogon Dawa, Damari, Saulawa da Farin Ruwa duk a ƙaramar hukumar Birnin Gwari.”
Bugu da ƙari, Mista Samuel Aruwan yace Dakarun sojin sun gudanar da bincike kan ababen hari masu ɗauke da makamai a fitacciyar hanyar nan mai hatsari da ta tashi daga Kaduna zuwa Birnin Gwari.
“Binciken ya kewaye garuruwan Buruku, Kurmin Dande, Damba, Ungwan Yako, Udawa, Manini, Kuriga, Gagafada, Kushaka, Polewire da Kamfanin Doka dake kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari, ba’a gano abin zargi ba.”
1 – Aruwan.
Daga karshe kwamishinan yace nan gaba kaɗan gwamnatin Kaduna zata sake fitar da ƙarin bayani kan nasarorin da zaran ta samu sabbin bayanai.
Sojojin Najeriya Sun Kashe ’Yan Bindiga da Dama a Wasu Manyan Dazukan Jihar Kaduna.
A wani labarin kuma Sojoji sun samu nasarar tura da yawan ‘yan bindiga barzahu a wasu sanannun dazuka masu hatsari a jihar Kaduna.
A wata sanarwa da gwamnatin Kaduna ta fitar, tace gwarazan Sojin sun kai samame dazukan Isasu, Fatika da Makera, kuma a bayanan da suka biyo baya an yi nasara mai girma.
Gwamnatin ta bakin kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ta roki al’umma su ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya da kai masu bayanan sirri.