Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan wata ganawarsa ta sirri da tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun ranar Lahadi.
A cewar wata sanarwa da kakakin tsohon shugaban kasa, Obasanjon, Kehinde Akinyemi, ya raba wa manema labarai a Abeokuta, ta ambato Lamido na cewa har yanzu tsohon Shugaban ya jaddada kwarin gwiwar sa kan Najeriya, duk kuwa da tarin kalubalen da ke fuskantarta.
Lamido ya ce, “Yadda za mu samu mu zauna lafiya yanzu shi ne babban kalubalen Najeriya, saboda yanzu babu wanda ya tsira.
“Ku duba fa wai har ma’aikatan gonar Baba [Obasanjo] ake sacewa a matsayinsa na tsohon Shugaban Kasa? Waye ya tsira kenan?” inji shi.
Tsohon Gwamnan ya ce ya je Jihar ta Ogun ne domin ya ziyarci Obasanjon a matsayinsa na uba kuma jagora, yana mai cewa ya same shi cikin karsashi da cikakkiyar lafiya.
Ya kuma ce, “Ya shaida min cewa yanzu tsufa ya cimmasa, amma na ce masa a’a, saboda har yanzu muna bukatarsa a kasar nan. Ya ce zai yi komai saboda Najeriya.
“Wannan abu ne mai karfafa gwiwa. Hakan na daya daga cikin dalilan da suka sa nake son shi, kuma ya kara karfafa imanin da nake da shi akan Najeriya
“Mun tattauna batutuwa da dama da suka shafi Najeriya, A zahirin gaskiya, ko ma ya muka tsinci kanmu, wata rana zai zama tarihi. Amma a yanzu dai kam tana kwararar jini.
A wani labarin na daban tashar Alkafil ta bayar da rahoton cewa, ana ci gaba da zaman karbar gaisuwar Ayatollah Sayyid Hakim Babban malami da Allah ya yi masa rasuwa a Iraki kwanaki tara da suka gabata.
Bayan ga zaman majalisin karbar gaisuwa a Najaf, ana wani majalisin a Karbala tsakanin hubbaren Imam Hussain (AS) da Abul Fadl (AS).
Ayatollah Sayyid Muhammad Said Hakim yana daga cikin manyan malaman mazhabar Ahlul bait (AS) wanda ya rasu a ranar Juma’ar wancan makon da ya gabata, sakamakon tsayawar zuciya.