Hedkwatar ‘yan sandan Najeriya ta aike da sabbin kwamishinonin ‘yan sandan jihohin Kano, Zamfara da Enugu.
A takardar mai lamba TH.5361/FS/FHO/ABJ/SUB.4/715, Lawal Abubakar aka tura Kano, Yusuf Kolo yana Zamfara sai Ahmed Ammani jihar Enugu.
Kamar yadda takardar ta bayyana, sabbin kwamishinonin ‘yan sandan zasu fara aiki a take ne bayan fitar takardar.
Hedkwatar ‘yan sandan Najeriya dake garin Abuja ta tura sabbin kwamishinonin ‘yan sanda jihohin Kano, Zamfara da Enugu.
Kamar yadda takardar mai lamba TH.5361/FS/FHO/ABJ/SUB.4/715 ta bayyana, an tura Abubakar Lawal jihar Kano yayin da aka aike Yusuf Kolo jihar Zamfara.
A takardar umarin, an bayyana cewa Ahmed Ammani ne ya zama sabon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Enugu.
Wadannan sabbin kwamishinonin ‘yan sandan zasu fara aiki a take ne, jaridar Daily Nigerian ta rahoto hakan.
Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, wanda aka dauko daga jihar Enugu, a wani lokacin baya shi ne DPO din yankin Hotoro dake jihar Kano.
A wani labari na daban, ‘yan Najeriya sun dinga martani kan rahoton dake bayyana cewa gagararren ‘dan bindiga Bello Turji, wanda ya saba kashewa da garkuwa da jama’a a Sokoto da Zamfara ya tuba.
Idan za a tuna, a watan Disamban 2021, shugaban ‘yan bindigan ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Bello Matawalle da Sarkin Shinkafi kan yana so a tsagaita da ruwan wuta.
A yayin jawabi a wani taro a Gusau a ranar Lahadi, mataimakin gwamnan jihar, Hassan Nasiha, ya bayyana cewa Turji ya tuba kuma ya rungumi matakan zaman lafiya na gwamnatin jihar.
Source: LEGITHAUSA