Jihohin Arewa guda bakwai sun ware tsagwaron kudi har Naira biliyan 28.3 domin ciyar da masu azumi a watan na Ramadan.
Jihohin guda bakwai sun hada da Katsina da Sakkwato, Kano, Jigawa, Kebbi, Neja da kuma Jihar Yobe.
Bayanai sun nuna cewa akwai wasu karin jihohin Arewac da dama da su ma suka ware kudaden domin ciyarwa.
Wannan abu dai ya janyo kace-na-ce a tsakanin mutane, inda wasu malaman addinin ke kira da a yi bincike bisa lura da irin yawan kudaden da aka ware.
Jihar Katsina ce dai ta fi kowace jiha kashe kudin, inda ta ware Naira biliyan 10.
Sai kuma jihar Sakkwato da ta ware Naira biliyan 6.7, sannan Jihar Kano da ta fitar da Naira biliyan shida.
Ita kuwa jihar Jigawa ta fitar da Naira biliyan 2.83, sai jihar Kebbi da ta fitar da naira 1.5 biliyan.
Jihar Neja ta ware naira miliyan 976, yayin da Jihar Yobe, ta ware Naira miliyan 178 domin ciyarwar.
A wani labarin na daban dakarun sojojin Nijeriya a jihohin Filato da Zamfara sun kubutar da wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su tare da kashe wani dan ta’adda.
A wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin kasar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce, sojojin da aka tura karamar hukumar Jos ta Kudu ta jihar Filato sun ceto wata Misis Rosemary Jekpe a kauyen Rafinbuna da ke karamar hukumar Bassa a jihar, bayan sun yi musayar wuta da masu garkuwa da mutane.
Ya ce, an yi garkuwa da matar ne a gidanta da ke Abuja Layout, Bukuru Low Cost Housing a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.
Ya ce, sojojin sun kuma kai wani samame kan wani da ake zargi da aikata laifuka a kauyen Zamtip da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato, bayan samun bayanan sirri.
Sanarwar ta kara da cewa, a yayin samamen da sojojin suka yi, sun cafke daya daga cikin masu laifin, yayin da wani kuma a yunkurinsa na tserewa kar a kama shi, ya kashe kansa.
A wani samame da aka yi a jihar Zamfara, rundunar sojojin a wani kiran gaggawa da aka yi musu, cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane Uku a wajen kauyen Kwatarkwashi da ke karamar hukumar Gusau.
DUBA NAN: Gobarar Dare Ta Kone Shaguna A Kumbotso Jihar Kano
Ya ce, sojojin sun yi artabu tare da fatattakar ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu sakin mutanen ukun da suka yi garkuwa da su, inda nan take sojojin suka ceto su.