‘Yan bindiga sun kashe mutane akalla 51 yayin jerin hare-hare da suka kai kan wasu kauyukan karamar hukumar Zurmi dake jihar Zamfara a Najeriya.
Rahotanni sun ce, garuruwan da ‘yan bindigar suka afkawa sun hada da Saulawa, Askawa, Kadawa, Kwata, Maduba, da kuma Ganda Samu.
Bayanai sun ce hare-haren sun tilasta wa daruruwan mutane da suka hada da mata da kananan yara tserewa zuwa cikin garuruwan Dauran da kuma Zurmi, inda a yanzu haka suke gudun hijira.
Wasu da suka tsira da rayukansu sun ce adadin ‘yan bindiga da dama ne haye kan babura suka afkawa garuruwan nasu, inda nan take suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
A wani labarin mai kama da wannan a jihar zamfaran sakamakon cigaba da tabarbarewar tsaro a Najeriya da kuma yadda Yan bindiga ke kashe mutane ba tare da kaukautawa ba, Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya bukaci jama’ar jihar da su kare kan su daga masu kai musu hari.
Gwamna Matawalle wanda a baya yace suna sasantawa da Yan bindigar domin ganin sun aje makaman su ya bayyana cewar lokaci yayi da za’a baiwa matasa damar kare yankunan su daga wadannan Yan bindigar dake kai muggan hare hare suna kashe mutane.
Yayin da yake jawabi wajen taron addu‘ar da akayi na cika shekaru biyu da hawa karagar mulkin sa, Matawalle yace Gwamnonin da suka fito daga Yankin arewacin kasar na wani shirin samar da tsaro a yankin wanda zai kunshi sanya hannu Sarakunan gargajiya wajen zabo irin mutanen da za’ayi amfani da su wajen kare yankunan su.
A wani shagube da yake yiwa abokan adawa, Gwamnan yace akwai mutanen dake farin ciki da hare haren da wadannan Yan bindigar ke kaiwa, kuma duk wanda yace babu hannun sa a ciki ya fito fili ya rantse da Allah kamar yadda shima yake yi.
Matawalle yace kare lafiya da dukiyoyin jama’a shine abinda ya saka a gaba, kuma zasu cigaba da rungumar duk hanyoyin da doka ta tanada wajen ganin sun dawo da zaman lafiya a yankunan da ake fama da tashin hankali.