Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 9 a kauyen Ba’are dake karamar hukumar Mashegu.
Kakakin rundunar Bala Kuryas wanda ya sanar da haka ranar Alhamis ya ce maharan sun kashe wadannan mutane ne ranar Laraba.
Kuryas ya ce an tura jami’an tsaro domin samar da tsaro a kauyen.
Mazauna kauyen sun ce mutum 16 ne aka kashe sannan 12 sun ji rauni.
Wani mazaunin kauyen da baya so a fadi sunan sa saboda tsaro ya ce ‘yan bindigan sun afka wa kauyen ne yayin da mutane ke sallah asuba ranar Laraba.
Ya ce wadanda suka ji rauni a jikinsu na asibitin Kontagora likitoci na duba su.
Idan ba a manta ba a watan Oktoba ‘yan bindiga sun kashe mutum 17 a masallacin dake kauyen Maza-Kula
‘Yan bindigan sun yi garkuwa da mutane da dama sannan wasu da dama sun ji rauni a wannan hari.
Sakamakon bincike ya nuna cewa mutane da dama a jihar sun zama ‘yan gudun hijira a cikin shekaru biyu da suka gabata a dalilin hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamnatin jihar ta ce a cikin shekara biyu mutum 151, 380 wanda mafi yawan su manoma ne sun zama ‘yan gudun hijira.
A karamar hukumar Mashegu mutum 2,010 ne suka zama ‘yan gudun hijira a cikin shekara biyu a jihar.