Jigon jam’iyyar APC, Sanata Magnus Abe ya ce ba zai taba goyon bayan Tony Cole ya zama Gwamnan jihar Ribas ba.
‘Dan adawan na Rotimi Amaechi ya ce babu abin da Cole ya tsinanawa APC tun da aka kafa ta Magnus Abe bai hakura da samun tikiti a APC ba, yana sa ran shi zai zama ‘Dan takara a 2023.
Babban jigon na jam’iyyar APC a Ribas da yankin Neja-Delta, Magnus Abe, ya shaida cewa ba zai marawa takarar Tonye Cole baya a zabe mai zuwa ba.
Da aka yi hira ta musamman da shi a gidan talabijin Channels a ranar Talata, Magnus Abe ya nuna ya ja layi tsakaninsa da ‘dan takaran APC na Ribas.
Sanata Abe wanda shi ma yana son kujerar Gwamna tun ba yau ba, ya ce Cole bai kai matsayin da jam’iyyar APC za ta tsaida shi a matsayin ‘dan takararta ba.
Tsohon Sanatan na Gabashin Ribas a majalisar dattawa ya ce sanannen abu ne cewa bai tare da Cole, domin ‘dan takarar na su bai da abin da zai iya nunawa.
A tattaunawar da aka yi da shi a shirin siyasa na Political Paradigm a Channels TV, Abe ya ce ba zai sa wa APC hannu a zaben gwamna da za ayi a 2023 ba.
An raba jiha a Ribas “A’a, ba zan goyi bayan Tonye Cole, ina tunanin kowa ya fahimci wannan.”
“Babu hannu na a yadda ya zama ‘dan takara, a iyakar sani na, bai cikin jam’iyyar mu, kuma bai bada gudumuwa wajen kafa jam’iyyar ba.”
“A tarihi, babu abin da ya tabuka a jihar mu (Ribas).” Wasu makudan kudi sun bace “Akwai zargin da ake yi na cewa sama da Dala miliyan 55 na dukiyar jihar Ribas sun shiga asusunsa ta hannun wajen Rotimi Amaechi”
Abe yake cewa ana zargin an tafka wannan badakala ne a mulkin Rotimi Amaechi, Abe ya yi aiki a gwamanatin, amma ya wanke kan shi daga zargin badakalar.
Da aka yi zaben fitar da gwani a watan Mayu, Sanata Abe bai yi nasarar samun takarar gwamna ba, amma har yanzu yana sa ran shi zai rike tutar APC a 2023.
APC ta tsaida ‘Dan takara a Sokoto Dazu aka ji labari ‘Dan takarar Gwamna a Sokoto, Ahmed Aliyu ya dauki Idris Muhammad Gobir ya zama ‘Dan takarar Mataimakin Gwamna a zaben 2023.
Baya ga Digiri shi da Idris Gobir ya ke da su, ya yi aiki Gwamnati, da a ofishin Ministan tarayya, kuma tsohon Kwamishina ne, har Kantoma ya rike a baya.
Source:hausalegitng