Abdulmumin Jibrin ya ce idan jam’iyyar NNPP ta hade da LP, to Rabiu Kwankwaso za a ba takara Tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayyan kasar yake cewa Kwankwaso ya fi Peter Obi sanin siyasa.
Hon. Jibrin ya ce ko a kasuwanci, duk wanda ya fi zuba hannun jari shi ne yake da kaso mai tsoka.
Tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya, Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa babu yadda za ayi Rabiu Musa Kwankwaso ya zama mataimakin Peter Obi.
A wata hira da gidan talabijin na Channels TV ta yi da Hon. Abdulmumin Jibrin, ‘dan siyasar ya yi magana game da hadin kan da ‘Yan NNPP ke neman yi da LP.
Abdulmumin Jibrin ya tabbatar da cewa akwai yunkurin da ‘dan takaran NNPP, Rabiu Kwankwaso yake yi na hada kai da Peter Obi na jam’iyyar LP.
Amma ‘dan siyasar ya fito baro-baro ya shaidawa shirin siyasar na Politics Today cewa muddin wadannan jam’iyyu za su dunkule, Kwankwaso ne za a ba tikiti.
Dalilan Jibrin na cewa a ba Kwankwaso tikiti “A zahiri Kwankwaso ba zai zama abokin takarar Peter Obi ba.
A kowane ma’auni aka duba, Kwankwaso ya kamata ya zama ‘dan takara.”
“Kwankwaso ya fi wayewa da kwarewa a siyasa. Ya fi yin suna idan aka zo maganar fice a siyasa. Shi ya fi sanin yadda za a bi wajen lashe zabe.”
‘Yan NNPP a taro Hoto: SaifullahiHon Asali: Twitter “A karshe idan aka duba gudumuwa ta fuskar kuri’u, za a samu kashi 70 da 30.
Mu ne za mu kawo kashi 70% na kuri’u idan aka shiga filin zabe.”
“Peter Obi ya san kasuwanci, ya san cewa wanda ya fi kawo kudi, shi yake da babban kasuwanci.”
Hon. Abdulmumin Jibrin Ibo za su goyi bayan NNPP?
A tattaunawar da aka yi da Jibrin wanda ya taba wakiltar mazabar Kiru da Bebeji daga jihar Kano, ya yi kira ga mutanen Kudu maso gabas su bi bayan Kwankwaso.
Jibrin yake cewa APC da PDP sun yaudari mutanen yankin, don haka ya nemi su hada-kai da jam’iyyar ta su NNPP wajen ganin sun kafa gwamnatin tarayya.
‘Dan siyasar yake cewa rabon Ibo da darewa kujerar mataimakin shugaban kasa tun 1979 zuwa 1983, sai a yanzu su ka samu babbar dama wajen jam’iyyar NNPP.
A cewar Jibrin, baya ga Obi, jam’iyyar NNPP ta na duba wani zabin na mataimakin shugaban kasa.
Tinubu ya na neman abokin takara Dazu kun ji labari Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yabawa kokarin da Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya taka wajen samun takarar shugaban kasa da ya yi a zaben APC.
Ganin har yanzu Tinubu bai gama lalube ba, shugaban majalisar wakilai ya ce a ba shi nauyin fito da ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023.