Tsohon ɗan majalisa kuma mai magana da yawun Kanfen din NNPP Jibril Abdulmumin ya ce sakamakon zaɓen 2023 zai kiɗima yan Najeriya.
Abdulmumini Jibrin ya ce babu jam’iyyar da zata samu kuri’u a jihar Kano, baki ɗaya na Sanata Rabiu Kwankwaso ne.
Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta tsayar da Kwankwaso a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023.
Mai magana yawun tawagar Kamfen ɗin jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Abdulmumini Jibrin, ya yi ikirarin cewa sakamakon zaɓen 2023 zai gigita ƴan Najeriya.
Tsohon ɗan majalisar ya faɗi haka ne yayin da yake tsokaci kan damar jam’iyyarsa na lashe zaɓen 2023 a wata hira da Channels tv cikin shirin ‘Siyasa a yau’.
Daily Trust ta ruwaito a kalamansa ya ce, “Ku rubuta ku aje, sakamakon zaɓen 2023 zai jijjiga yan Najeriya, duk abin da ke shirin faruwa nan da watanni shida ba zai wa PDP da APC daɗi ba.
Jam’iyyar NNPP ce zata ci gajiyarsa.”
“Babu wata haɗin guiwa da NNPP ko Kwankwaso ke bukata, idan kana son mu haɗa karfi da kai a shirye muke, amma ka sani mu ke da mafi rinjayen kuri’u.”
“Idan ka duba yadda muka gudanar da zabukan fidda gwanin mu bamu bar ko wace kafa da zata bamu matsala ba kamar yadda kuke gani yanzu, jam’iyyu na ta aibata junan su.”
Ba Jam’iyyar da zata samu kuri’u a Kano – Jibrin Jibrin ya ƙara da cewa jam’iyyar All Progressive Congress APC da PDP na ta fafutukar samun kaso 25% a kuri’un jihar Kano amma ba zai yuwu ba.
“Mun ji labarin cewa APC da PDP na ta faɗi tashin yadda zasu sami kashi 25% na ƙuri’un Kano duk da sun san ba zasu ci jihar ba amma a lissafin su idan suka tsakuri nan da can zasu iya kai labari.”
“Bari na faɗa muku wata magana, babu wata jam’iyya da zata sami 25% a Kano, zamu tarkata baki ɗayan su ga Kwankwaso kamar yadda na faɗa a baya da kuri’u miliyan biyar.”
A wani labarin kuma Hotunan Yadda Tinubu, Shettima da Adamu Suka Fara Kulle-Kulle a Abuja Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da Sanata Kasshim Shettima, sun yi wata ganawa ta dabaru da wasu jiga-jigan jam’iyya a Abuja.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, na daga cikin mahalarta taron tare da wasu mambobin kwamitin gudanarwa.