Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi wa fitaccen malamin addini, Apostle Jerry Hinjari, kisar gilla a Adamawa.
A cewar rahotanni, an kashe babban faston na Christ Nation International ne tsakanin ranar Laraba da Alhamis bayan an sace shi daga gidansa da ke babban birnin jihar.
A bangare guda, rundunar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da afkuwar lamarin na bakin ciki bayan gano gawar malamin addinin a gefen titi a ranar Alhamis.
An kashe fittacen faston Najeriya, Apostle Jerry Hinjari a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
A cewar Sahara Reporters, an halaka Hinjari, babban faston Christ Nation International ne tsakanin ranar Laraba da Alhamis bayan an sace shi daga gidansa da ke kusa da Eagles Path, Army Barracks Road, a Yola, babban birnin jihar.
Yan uwansa sun yi martani Da suke martani kan abin bakin cikin, wani daga cikin dangin mammacin wanda ya yi magana da Sahara Reporters amma ya nemi a boye sunansa ya ce: “Yan bindigan sun tafi gidansa misalin karfe 11 na dare zuwa 12 a ranar Laraba suka tafi da shi.”
Lokacin da suka kutsa dakinsa, ya bukaci su ambaci duk adadin kudin da suke so zai basu; amma ba su ce komai ba, amma, suka tafi da shi.
“Mun tsinci gawarsa a ranar Alhamis da rana kusa da sansanin yan gudun hijira na Malkhohi, hanyar Mayo-Ine.”
Yan sanda sun yi martani
A bangarensu, rundunar yan sandan jihar Adamawa sun tabbatar da afkuwar lamarin ta bakin kakakinta SP Yahaya Nguroje.
Ya ce: “Zan iya tabbatarwa cewa an sace shi (Hinjari) a ranar Laraba kuma an gano gawarsa goben ranar.”
A halin yanzu, kwamishinan yan sanda, Sikiri Akande yana jogarantar bincike don gano wadanda suka aikata wannan mummun abin.
Muna tabbatarwa mutanen kirki na jihar cewa za a hukunta wadanda suka aikata abin.”
An cafke wasu sojoji biyu da ake zargi da halaka babban malamin addinin musulunci Sheikh Aisami a Jihar Yobe Kun ji cewa yan sanda a jihar Yobe sun kama wasu jami’an sojoji biyu da ake zargi da hannu wurin kashe babban malamin addinin islama Sheikh Goni Aisami da aka halaka a ranar Juma’a kamar karfe 9 a hanyarsa ta komawa Gashuwa.
A cewar majiyoyi da dama, sojojin da ake zargi sun halaka malamin addinin ne bayan ya dauke su a hanya daga Nguru zuwa garin Jaji-Maji da ke karamar hukumar Karasuwa a Jihar Yobe.