Mun kawo jerin duk wanda suka taba rike mukamin Alkalin Alkalai a Najeriya Adetokunbo Ademola shi ne ya fi kowa dade wa a ofis, ya kusa shekara 15 a kujerar.
A jerin akwai irinsu Taslim Olawale Elias wanda ya yi Ministan shari’a na kasa.
Burin duk wani babban Alkali ya zama Alkalin Alkalai na kasa. Alkalin Alkalai wanda ak fi sani da CJN shi ne shugaban bangaren shari’a na kasa.
Shugaban kasa yana zaben babban Alkalin kotun koli a matsayin shugaban Alkalai bisa shawarar NJC.
Dole majalisar dattawa ta tantance shugaban Alkalan.
Sannan sai da sa hannun mafi yawan ‘yan majalisa dagoyon bayan majalisar shari’a NJC ne za a iya sauke CJN, ko kuma idan har ya cika shekara 70 a Duniya.
A halin yanzu Mai shari’a Ariwoola ne Shugaba Buhari ya rantsar yau kan wannan kujera.
Daga baya aka tursasa wa Walter Onnoghen ya ajiye mukaminsa saboda wasu zargi da ke kansa.
Mahmud Mohammed, Dahiru Mustafa, Aloysius Katsina-Alu, Idris Kutigi, Salihu Belgore, Lawal Uwais da Mohammed Bello sun rike kujerar na shekaru 27. A shekarar 2012 aka samu macen da ta zama CJN.
Shugaban kasa na wancan lokaci, Goodluck Jonathan ya nada Aloma Maryam Mukhtar, ta sauka a 2014.
Adetokunbo Ademola, Mohammed Bello, da Muhammad Lawal Uwais sune su ka fi dade wa a ofis. Kafin Ademola, Birtaniyawa ne suka yi ta rike kujerar CJN.
Legit.ng Hausa ta tattaro ‘yan kasa da suka taba zama shugabannin Alkalai a tarihin Najeriya. Mun tsakuro wasu daga cikin bayanan ne daga shafin Wikepedia.
1. Sir Edwin Speed, 1914–1918
2. Sir Ralph Combe, 1918–1929
3. Donald Kingdon, 1929–1946
4. Sir John Verity, 1946–1954
5. Sir Stafford Sutton, 1955–1958 Zamanin mulkin Soja
6. Sir Adetokunbo Ademola, 1958–1972
7. Taslim Olawale Elias, 1972–1975
8. Sir Darnley Arthur Alexander, 1975–1979
9. Atanda Fatai Williams, 1979–1983
10. George Sodeinde Sowemimo, 1983–1985
11. Ayo Gabriel Irikefe, 1985–1987
12. Mohammed Bello, 1987–1995 Bayan Mulkin Soja
13. Muhammad Lawal Uwais, 1995–2006
14. Salihu Moddibo Alfa Belgore, 2006–2007
15. Idris Legbo Kutigi, 2007–2009
16. Aloysius Iyorgyer Katsina-Alu, 2009–2011
17. Dahiru Musdapher, 2011–2012
18. Aloma Mariam Mukhtar, 2012–2014
19. Mahmud Mohammed, 2014–2016
20. Walter Samuel Nkanu Onnoghen, 2017–2019
21. Ibrahim Tanko Muhammad, 2019–2022
22. Olukayode Ariwoola, 2022
Source:legithausang