Wani dan Najeriya mai suna Sir Jarus ya yada wani rubutu a Twitter, ya bayyana yadda karatu ke da sauki a shekarun baya karkashin karkashin.
A cewarsa, ya tuna yadda ya biya N40 a matsayin kudin makaranta JSS1 a 1994 kana ya kashe N1,090 a matsayin kudin rajistar shiga jami’a, har da wurin kwana a 2001.
Ya ce, dukkan kudin da ya kashe daga Firamare zuwa kammala digiri bai kai N200k ba, kudin shiga wata jami’ar a yanzu.
Wani dan Najeriya mai suna Sir Jarus ya yada adadin kudaden da ya kashe na yin karatun boko a rayuwarsa; daga firmare zuwa jami’a.
A cewarsa, ya taba biyan kudin rajistar shiga karamar sakandare JSS1 N40 a shekarar 1994.
Hakazalika, ya ce lokacin da ya kammala sakandare, ya shiga jami’a a 20221, kuma kudin da ya kashe na rajista da kudin wurin kwana a shekarar gaba daya N1,090 ne.
Ban Kashe ya Kai N200K ba Tun Daga Firamare har Jami’a: ‘Dan Najeriya ya Bayyana Rasit din Kudin Makarantarsa Ya kara da cewa, a ajin karshe a jami’ar da ya yi ta Obafemi Awolowo, N15,000 kadai ya kashe.
Ya kara da cewa, dukkan kudin da ya kashe tsakanin Firamare da Jami’a bai kai N200,000 ba idan za a hada.
Ya rubuta: “Zangona na farko a JSS1 kudin makaranta N40 (Naira arba’in ne) a shekarar 1994.
Na biya N1,090 (Naira duba daya da Naira casa’in) a matsayin kudin rajistar shiga jami’a aji daya da wurin kwana a shekarar 2001. “Na biya 15k ko makamancin haka a ajin karshe.
Dukkan kudin da aka kashe a karatuna daga firamare zuwa jami’a
“Na biya 15k ko makamancin haka a ajin karshe. Dukkan kudin da aka kashe a karatuna daga firamare zuwa jami’a kasa da 200k ne.