Taurauruwar shirin Labarina mai dogon zango, jaruma Nafisa Abdullahi, ta sanar da ficewarta baki daya daga cikin shirin Jarumar ta alakanta ficewarta daga shirin da kasuwancinta, makaranta da kuma wasu fina-finanta da ta ke shirin fara dauka Nafisa kuma Sumayya a shirin, ta mika godiya da fatan alkhairi ga masoyanta da Saira Movies inda tace za a cigaba da shirin ko babu ita.
itacciyar jarumar Kannywood kuma tauraruwar shiri mai dogon zango na Labarina, Nafisa Abdullahi, ta sanar da ficewarta gaba daya daga shirin fim din.
Tun farko, an yi makonni ba a ga jarumar ta bayyana cikin shirin ba sakamakon yadda wasan ya zo na cewa an yi garkuwa da ita, lamarin da yasa masoyanta suka dinga guna-gunin rashin bayyanarta.
Jaruma Nafisa Abdullahi ta sanar da ficewa daga fim din Labarina, ta sanar da dalilanta.
Sai dai a ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara, jaruma Nafisa Abdullahi ta wallafa takarda a shafin ta na Instagram inda ta sanar da cewa ta fice daga shirin sakamakon tarin ayyukanta da karatu da ya sha mata kai.
Jaruma Nafisa Abdullahi ta sanar da cewa fim din Labarina ya na daga cikin ayyukanta da ta ke alfahari da shi kuma kamfanin Saira Movies tamkar na ta ne saboda ta dade ta na aiki da kamfanin.
Kamar yadda ta ce: “Aikin Labarina aiki ne da nake alfahari da shi a duk inda na shiga.
Kamfanin Saira Movies kuwa tamkar kamfanina ne saboda mun jima muna aiki tare. “Ina matukar jin zafin sanar da dukkanku cewa ba zan cigaba da aikin Labarina ba.
Dalili shi ne rashin samun lokaci yadda ya kamata. Ina da kasuwanci na, makaranta, kamfanina da sauran fina-finai na da nake shirin fara dauka nan babu dadewa.
“Ba zan ce a jira ni sai sanda na samu lokaci ba, dole za a cigaba da shirin Labarina ko da ni ko ba ni.
“Ina ba dubban masoya hakuri a kan fita ta daga shirin.
Alakata da Saira Movies za ta cigaba da tafiya lafiya, babu hayaniya ko cin zarafi. Allah kuma ya ba su sa’a wajen kammala sauran shirin.”
A wani labari na daban, Shatu Garko, Sarauniyar kyau ta 44 a Najeriya ta shaida yadda ta samu nasarar shawo kan mahaifinta har ya amince ta shiga gasar.
Budurwar mai shekaru 18 ta zama mace ta farko mai hijabi da ta kashe gasar tun da aka fara a shekarar 1957 kamar yadda ta shaida wa The Punch a wata hira da jaridar ta yi da ita.
Kamar yadda tace: “Mahaifiyata dama tana goyon bayana kuma ta na nuna min ba wani abu mai wahala bane, amma mahaifina ne baya so.”