Jam’iyyar APC ta buƙaci Shugaba Buhari ya mutunta umarnin kotu kan wa’adin tsofaffin kuɗi
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sake tsunduma cikin ruɗani da rabuwar kawuna, inda shugabancin jam’iyyar ya bi sahun wasu gwamnonin ƙasar da ke fito-na-fito da manufar daina karɓar tsoffin kuɗi ta Shugaba Muhammadu Buhari.
Bayan wani taro da Kwamitin Gudanarwar APC na kasa ya gudanar da yammacin jiya Lahadi, jam’iyyar mai mulki ta yi kira ga shugaban ƙasar ya mutunta umarnin Kotun Ƙoli a kan wannan batu.
Taron wanda mahalartansa suka shafe kimanin tsawon sa’a biyar suna tattaunawa a hedikwatar APC ta ƙasa, ya kammala ba tare da wani dogon bayani kan yadda al’amura suka kaya ba.
Sai dai fuskokin gwamnonin APC da suka halarci taron, babu annuri.
Haka zalika, sanarwar bayan taro da shugaban APC na ƙasa ya karanta bayan fitowarsu, taƙaitacciya ce.
Wannan kuwa na zuwa ne adaidai lokacin da yake kwanaki kalilan a gudanar da babban zaɓe. Sannan al’umma na kokawa da yanayi matsin rayuwa da batun sauya kudi ya jefa su.
Batutuwan da taron ya tattauna
Jam’iyyar APC dai ta goyi bayan matsayin gwamnoninta a kan shugaban ƙasa game da dambarwar canjin kuɗin.
Shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya ce sun lura da cewar sabon tsarin canjin takardun kuɗin da gwamantin kasar suka kawo, ya jefa ‘yan kasar cikin mawuyacin hali.
Sannan suna kira ga gwamnan Bankin Najeriya wato CBN da ministan shari’ah na tarayya, su girmama umarnin da kotun ƙoli ta bayar tun farkon zamanta na a dakata har sai ta yanke hukunci.
Sannan kuma Shugaban APCn na ƙasa, ya ce shugabancin jam’iyya da gwamnonin sun cimma matsaya, a kan Shugaba Buhari ya sa baki game da halin da ake ciki.
Cikin mahalarta taron na yammacin jiya Lahadi, an ga fuskar ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar wato Bola Ahmad Tinubu a ofishin jam’iyyar.
Kimanin gwamnoni 10 da mataimakan gwamna 2 ne suka halarci taron, da shugaban jam’iyyar ta APC mai mulkin ƙasar ya kira, sai dai duk sun ƙi cewa komai kan abin da suka cimma.
Ɓaraka a jam’iyyar APC
Matakin na jam’iyyar APC ta Shugaba Buhari, na zuwa ne daidai lokacin da ɓaraka tsakanin gwamnatinsa da wasu gwamnonin kasar ke daɗa ƙamari.
A baya-bayan nan dai rahotanni sun sake ambato gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufa’i yana bai wa hukumomi da ma’aikatu a jiharsa umarnin su ci gaba da hada-hada da tsoffin takardun kuɗi na naira dari biyu da ɗari biyar, da kuma dubu ɗaya.
Yayin da bayanai ke cewa gwamnonin sun sake ɗunguma zuwa wani taron, da ake sa ran zai iya shafe tsawon dare duk dai kan wannan dambarwa.
Da wuya dai a iya cewa ga inda wannan lamari, zai kai jam’iyyar APC mai mulki da ma Najeriya gaba ɗaya. Ƙasa da kwana biyar a shiga rumfunan babban zaɓen ƙasar.
Kalaman shugaba Buhari kan halin da ake ciki
Shugaba Muhammadu Buhari ya nanata ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da yin zaɓukan da za a fara a ƙarshen wannan mako, inda ya ce an ɗauki dukkan matakai don tabbatar da nasara.
A cikin wani saƙon bidiyo da shugaban ya aike ga ‘Yan Nijeriya daga ƙasar Habasha inda yake halartar taron ƙolin Tarayyar Afirka, Shugaban ya buƙaci ‘yan ƙasar su ƙara haƙuri kan wahalhalun da suke ciki game da batun canjin kuɗi.
Ya ce; “Allah ya sake kawo mu wani lokaci na babban zaɓe a faɗin ƙasa. Don haka ina kiran dukkanku, ku yi amfani da ‘yancinku na zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana”.
“Ina kira ga taƙamaimai sarakuna da malaman addinai da iyaye, su gargaɗi mabiya da ‘ya’yansu kada su bari wasu mutane ‘yan ƙalilan su yi amfani da su wajen haddasa tashin hankula.
“Ina so na ba ku tabbacin cewa gwamnati ta ɗauki isassun matakan tsaro da za su bai wa kowa damar fita su kaɗa ƙuri’unsu.”
Shugaban na Najeriya ya kuma tabbatarwa ‘yan kasar cewa yana da cikakkiyar masaniya game da halin matsin da suke ciki yanzu haka saboda wasu manufofin gwamnati waɗanda ke da nufin inganta ɗaukacin al’amuran rayuwa a ƙasa, in ji shi.
“Ina roƙonku, ku daɗa haƙuri, yayin da muke ɗauƙar matakan da suka dace don kawo sauƙi ga waɗannan wahalhalu.
“Insha Allahu, akwai sauƙi a ƙarshe”, in ji Buhari.
Sharhi
‘Yan Najeriya dai kusan a yanzu sun shiga yanayi na rashin zaɓi la’akari da matsatsin da ake ciki.
Galibi dai mutane na kokarin ganin su kirkiri hanyar samun mafita ko waraka.
Ko da yake akwai da dama da ko sayen abinci ke gaggararsu saboda wannan manufa ta sauya kuɗi.
Duk da cewa a gefe guda gwamnati na cewa tayi hakan ne domin inganta rayuwa da bukasa tattalin arziki, mutane da dama na ɗiga ayar tambaya kan lokacin da za a farfaɗo daga wannan kangi.
Masana tattalin arziki dai na ganin akwai rashin dabbara a wannan tsari, yayinda kalilan ke cewa wannan wani salo ne kawai na hana sayen kuri’a a zaɓen da ke tafe.