Jam’iyyar APC A Najeriya Za ta Zabi Dan Takarar Shugaban Kasa A Watan Mayu.
Sakataren jam’iyyar, Iyiola Omisore ne ya saka hannu a takardar da jam’iyyar ta aika wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC. Idan ba a manta ba hukumar zaɓe ta umarci jam’iyyun kasar nan su tabbata sun yi zaɓen fidda gwani da kuma aika wa da sunayen yan takarar kujerun su a farkon watan Yuni.
APC ta ce za ta gudanar da zaben wanda zasu tsaya takara a kujeran gwamna a jihohi a ranakun 23 da na majalisar jihohi kuma a ranakun 11 ga Mayu. Sai kuma na kujerun majalisar tarayya da na dattawa a ranar 18 ga Mayu.
Jam’iyyar za ta gudanar da babban taron tan a kasa a ranar Laraba mai zuwa wand shi ne taro na farko da za ta yi a ƙarkashin sabbin zababbun shugabannin ta da aka yi a watan Maris.
READ MORE : Iran Za ta Ci Gaba Da Rike Kyamarorin Hukumar Nukiliya Har Sai An Rattaba Hannu.
Wadanda za a fafata a tsakanin su a neman kujrar shugabancin kasar karkashin iunwar Jamiyar APC kuwa sun haɗa da Bola Tinubu, Rotimi Amaechi, Rochas Okorocha,David Umahi, Orji Uzor Kalu, Yahaya Bello, da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.