Hukumar gudanarwar jami’ar Modibbo Adama, da ke Yola, ta kori wani dalibinta mai suna Salihu Usman da ya fito daga yankin karamar hukumar Ganye a jihar Adamawa.
Salihu Usman da yake zangon karatu na biyu, jami’ar ta ce ta gano cewa ya shigo ne da takardar jarrabawa ta NBAIS, wato shaidar Hukumar Jarrabwa ta Nazarin Larabci da Ilimin Islama.
Rahotanni sun nunar da cewa, Jami’ar Modibbo Adama, Yola, ba ta tashi gano hakan ba, sai da Salihu Usman ya kai zangon karatu na biyu, yayin da ya yi wa ‘yan ajinsu fintinkau a jarrabawarsu ta zangon farko da ta biyu.
Bayanan sakamakon jarrabawar Salihu sun nuna ya samu maki a ma’aunin karatu na jami’a da CGPA 4.47, a jarabawar zangon farko, ya kuma samu 4.18 a zangon jarrabawa na biyu.
An kori Salihu Usman ne biyo bayan kafa kwamitin tantance takardunsa da jami’ar ta yi inda kwamitin ya tabbatar da cewa da takardun jarrabawar NBAIS, ya shigo jami’ar.
Binciken wakilinmu ya gano cewa Salihu Usman ya yi jarrabawar JAMB ta kasa wacce ake yi da Turanci, ya samu makin da Jami’ar Modibbo Adama take bukata kuma aka dauke shi domin yin karatun Digiri. Sai dai hakan bai sa kwamitin la’akari da kwazon da Salihu Usman ya nuna a jarrabawa ba, ya bayar da shawarar korar shi.
A ranar 13 ga Disimbar 2023, hukumar jami’ar ta ba shi takardar kora mai lamba MEU/R/ACA/S.5/BOL.1, wacce Malama A.K. Mohammed, ya rattaba wa hannu a madadin magatakardar jami’ar.
Salihu Usman dai ya yi karatunsa ne a cibiyar Nazarin Larabci da Ilimin Addini ta ‘Atiku Abubakar Center for Arabic and Islamic Studies’ da ke Ganye, a Karamar Hukumar Ganye a Jihar Adamawa, kuma a makarantar ya yi jarrabawar NBAIS da JAMB.
Ganin kwazonsa, ya sa shugaban makarantar, Malam Kabiru Sa’ad, ya sanar da Malam Muhammadu Sani Jada wanda daya ne daga cikin jiga-jigan kafa makaratun cibiyar ta Atiku da ke Ganye, Jada, Toungo da Kojoli fiye da shekaru ashirin, halin da ake ciki.
Malam Sani Jada bai yi kasa a gwiwa ba, ya karbi takardun Salihu Usman ya rubuta wa NBAIS wacce ke da hidikwata a Kaduna, kuma ya yi tattaki ya je Kaduna, ya fargar da shugabannin NBAIS hadarin da ke tattare da nuna halin ko oho da rashin daukar daliban da suka zana jarrabawar NBAIS da jami’o’in Nijeriya musamman ma dai ga Jami’ar Modibbo Adama Yola ta kori wanda JAMB ta dauka bayan har ya fara karatu.
Malam Sani Jada ya kara shaida wa NBAIS cewa, idan aka kyale wannan halin ya ci gaba; to kuwa dalibai za su kaurace wa jarabawar NBAIS baki-daya a Nijeriya, wanda kuma hakan ya tabbatar da nuna cewa, NBAIS ta kama hanyar mutuwa kenan kacokan.
Takardar da Malam Sani Jada ya rubuta wa NBAIS, ya kuma aike wa Ministan Ilmi; Farfesa Tahir Mammam (SAN) da kuma Hukumar Gudanar da Jami’o’i ta kasa (NUC) da ke Abuja.
Tuni dai Ministan Ilimin ya umarci Jami’ar Modibbo Adama Yola da ta rubuta wa Malam Muhammadu Sani Jada cikakken bayanin dalilin korar Salihu Usman daga jami’ar, bayan da jami’ar ta rubutu bayanin ne ta ce wai “ta dauki Salihu Usman ne bisa kuskure” (ERROR).
A wasikar martinin da Malam Muhammadu Sani Jada ya yi wa jami’ar ta Modibbo Adama, ya bayyana mamakin yadda jami’a za ta dauki dalibi bisa kuskure, ya ce dalibi ya yi rigista ta shiga ajin farko bisa kuskure, ya biya duk kudaden da jami’ar ta ayyana bisa kuskure, ya shiga aji har na tsawon zangon karatun farko bisa kuskure, ya yi jarrabarwar farko bisa kuskure, ya samu makin CGPA 4.47 duk ba’agano kuskuren ba.
Ya kara da cewa, dalibi ya sake dawowa zango na biyu ya yi rigista ya biya duk kudaden da jami’a ta ayyana domin karatun zangonsa na biyu, ya shiga aji ya yi jarabawar zango na biyu; har ya sake yi wa ‘yan ajinsu fintikau da makin CGPA 4.18 duk dai bisa kuskure, sannan aka gano cewa; wai Salihu Usman bai cancanta ya yi karatu a jami’ar ba.
Saboda haka, sai aka nada masa kwamitin da ya bayar da shawarar a kore shi, aka kuma kore shin daga jami’ar, ya ce indai haka ne wannan kuskure ya wuce kuskure; ya kai ga zama ganganci da rashin sanin makamar aiki.
Ya kara da cewa, indai har jami’a za ta dauki dalibi ta binciki takardunsa ta amince masa ya rika shiga aji har na tsawon zangon karatu (first semester) ya kuma yi jarrabawar wannan zangon karatu; ya samu CGPA 4.47, ya sake dawowa ya yi rigistar zango na biyu (second semester), sai sannan ne jami’a za ta gano dalibin ya shigo ne da takardun NBAIS, don haka ta kore shi; a kuma aiwatar da korar a ranar 13 ga watan Disamba, 2023, lallai kuwa akwai lauje cikin nadi.
Masu lura da abin da kaje ya dawo sun nuna cewa, ko shakka babu wannan kora akwai walakin Goro a Miya, bayan samun takarda da Malam Muhammdu Sani Jada ya yi, ya tura wa Ministan Ilmi Farfeso Tahir Mammam (SAN), inda ya umarci hukumar jami’o’i ta kasa (NUC) ta rubuta wa daukacin jami’o’in Nijeriya wasika kan cewa, jarrabawar NBAIS ingantacciyar jarrabawa ce, sannan kuma ta na da daraja kai daya da ‘O’ lebel’, kuma za ta bai wa duk wani dan Nijeriya damar shiga kowace irin jami’a.
Daga bisani, ofishin Ministan Ilmi Farfesa Tahir Mammam (SAN), a ranar 26 ga watan Fabrairun 2024; ta rubuta wa Shugaban Jami’ar Modibbo Adama Yola, takarda mai lamba FME/TE/SU/55A/T3/296, inda ta umarci jami’ar da ta janye takardar korar Salihu Usman tare da mayar da shi jami’ar, domin ci gaba da karatunsa nan take.
Umarni na biyu kuma shi ne, sauran daliban da Hukumar JAMB ta bai wa takardun amincewa, har ta ba su gurbin karatu da jami’ar Modibbo Adama Yola ta hana su; da ta tabbatar ta nemo su ta ba su guraben karatu ba tare da wani baba lokaci ba.
Binciken wakilinmu ya tabbatar da cewa, jama’ar yankin Kasar Ganye da kuma dukkanin Makarantun da ke mu’amala ta jarrabawa da NBAIS, sun yi matukar murna da farin ciki tare da jinjina wa Ministan ilimi; Farfesa Tahir Mammam (SAN), dangane da namijin kokarin da ya nuna a matsayinsa na Ministan Ilmin Nijeriya, domin kuwa matakin da ya dauka ya nuna za a kare hakkin dan talaka, domin shi ma ya samu damar yin karatu a manyan makarantun kasa.
A lokacin da wakilinmu ya samu ganawa da Salihu Usman, dalibin da Jami’ar ta Modibbo Adama Yola ta kora, cewa ya yi; jami’ar ta mayar da shi nan take, ya kara da cewa; jami’ar ta rubuto masa da takarda mai lamba MAU/R/ACA/S.5/BOI.1, a ranar 27 ga Fabrairun 2024 tare da sa hannun A.K Mohammed, wacce ke nuni da janye waccan kora da ta yi masa.
Da wakilinmu ya tuntubi Malam Muhammadu Sani Jada, kan batun cewa ya yi, “na gode wa Allah da ya taimake ni ya kuma ba ni ikon jajircewa da nema wa wannan dalibi dan talaka mai hazaka Salihu Usman ‘yancinsa na komawa makaranta don ci gaba da karatu.
“Ina kira ga Shugabanin Jami’ar Modibbo Adama Yola, da su rika yin adalci tare da samar da sashin da zai rika bai wa dalibai shawara, kan kwasa-kwasan da su ke son yin karantu a kansa, tun lokacin da dalibi ya shiga jami’ar, ba sai lokacin da yaro ya fara karatu ya wahala, iyayensa su ma suka wahala; sannan kuma sai a ce wai an sami kuskure (ERROR) a kore shi daga jami’a ba”, in ji Jada.
Al’ummar Masarautar Ganye, sun yi Allah san barka da wannan yunkurin da dansu Muhammadu Sani Jada ya yi, domin ya ceto dansu daga zama guda cikin zauna-gari-banza.
DUBA NAN: Matsalar Dake Tattare Da Fasa Runbunan Abinci
Yanzu haka dai, ya tabbata cewa Cibiyar Jarrabawar NBAIS; na daya daga cikin cibiyoyin zana jarrabawar shiga jami’o’i da sauran manyan makaratun Nijeriya.
Binciken LEADERSHIP HAUSA ya gano cewa, iyayen Salihu Usman, sai da suka sayar da gonarsu ta gado, kafin su kai ga samun damar biya wa dan nasu kudin shiga wannan jami’a ta Modibbo Adama da ke Yola.