Hukumar gudanar da Jami’ar Maryam Abacha American University of Niger (MAAUN), ta taya daya daga cikin Malamanta Dr. Mahmud Muktar Sorondinki ta’aziyyar rasuwar dansa Aminu Mahmud.
Dr. Mahmud Muktar Sorondinki ya kasance Malami ne a sashen koyar da ilimin bin diddigin kudi (Accounting) na jami’ar.
Aminu Mahmud, dan shekara 18 ya rasu ne a ranar Asabar 10 ga watan Yulin 2021.
Sakon ta’aziyyar na dauke ne da sa hannun shugaba kuma mu’assasin Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Litinin.
Hukumar gudanar da Jami’ar ta bayyana rasuwar Aminu a matsayin wani babban rashi ga mahaifinsa, iyalinsa da kuma dukkanin ma’aikatan jami’ar Maryam Abacha American University dake jamhuriyyar kasar Nijer.
Takardar ta kara da cewa; “shugaba kuma jagoran Jami’ar Maryam Abacha American University dake Nijer da Nijeriya, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo a madadin hukumar gudanarwa muna mika sakon ta’aziyya da alhini ga Dr Mahmud Muktar Sorondinki da dukkanin iyalinsa bisa wannan babban rashin”.
A karshe Fafesa Abubakar Gwarzo ya yi addu’ar Allah ya jikan mamacin, ya kuma sanya shi a madaukakiyar aljannah ta Firdaus.