Shafin jaridar Al-ahad ya bayar da rahoton cewa, jami’an ‘yan sanda na masarautar Saudiyya sun kai farmaki a kan masu tarukan juyayin dararen Muharram na Ashura a yankin Qatif da ke gabashin kasar.
A yayin kai farmakin da jami’an suka kai an kame mutane da suka hada har da limaman masallatai da kuma wasu daga cikin malamai masu gabatar da jawabai kan hakikanin abin da ya faru da zuriyar manzon Allah (SAW) a tarihi a cikin irin wadannan ranaku na goman farko na watan Muharram.
An saki wasu daga cikin limaman bayan cin su tara ta kudi da bai gaza riyal dubu 60 ba a kan kowanensu, tare da yin barazana a kansu matukar dai suka sake gudanar da irin wadannnan taruka ko kuma jawabai a kan wadannan ranaku na Muharram.
Wannan dai ba shi ne karon farko da hakan ke faruwa a kan mutanen yankunan gabashin kasar Saudiyya ba, wadanda akasarinsu mabiya mazhabar ahlul bait (AS) ne da suke raya duk wani lamari da ya shafi manzon Allah (SAW) ko kuma alayen gidansa.
An dai shaidi jami’an tsaron saudiyya da tsananin musgunawa ‘yan kasa.
A wani labarin na daban tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Gwamnatin Saudiyya ta haramta wa ‘yan kasashe 33 gudanar da ayyukan ibadar Umrah saboda dalilai na kiwon lafiya.
Rahoton ya ce, mai yiwuwa gwamnatin kasar ta Saudiyya ta fitar da jerin sunayen a hukumance ga kafofin yada labarai.
Sai dai tuni shafin almisrawi ya fitar da sunayen wasu daga cikin wadannan kasashe, da suka hada da Amurka, Masar, Afirka ta kudu, Italiya, Faransa, Switzerland, Ingila, Swden, Jamus, Argentina, Brazil, Japan, China, Turkiya, India, Indonesia, Pakistan , Iran, Liberia, Gunea Bissau, Portugal, Armenia, Lebanon, Hadadiyar Daular Larabawa da sauransu.
A nata bangaren ma’aikatar kula da harkokin aikin hajji da Umrah ta sanar da cewa, ta sanar da sauran kasashe cewa an bude kofar ayyukan umrah, amma dukkanin mutanen da za a iya karba daga kasashen da amince zuwansu ba zai wuce mutane dubu 60 ba a baki daya.
A daya bangaren kuma a karon farko an nada mata guda biyu ga shugaban hukumar da ke kula da haramomi biyu masu alfarma na Makka da Madina.