Jami’an Diplomasiya A Kasar Burkina Faso Sun Sha Alwashin Taimakawa Wajen Dawo Da Tsaro.
Jakadan kasar China a kasar Burkina Faso Li Jian shi ne ya fiar da wannan sanarwar a madadin sauran jami’an jiya diplomasiya a kasar Burkina Faso bayan wata ganawa da suka yi a jiya juma’a da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar, domin duba hanyoyi da zasu taimaka musu wajen tunkarar kungiyoyi masu ikirarin jihadi a kasar
Har ila yau jakadan na kasar china dake wakiltar kasar a kungiyar tarayyar turai da kasar faransa da kuma kasar Mali ya kara da cewa taron ya gudana ne domin dubi yadda zamu bada tamu gudunwamar wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar bayan kifar da gwamnatin farar hula
Wanda ya jagoranin juyin mulkin Paul Henri Sandaogo Damiba ya fadi cewa sun kifar da gwamnatin shugab Kabore ne saboda damuwar da alummar kasar ke nunawa game da yadda gwamnati ke sakwasakwa wajen shawo kan matsalar tsaro da kasar ke fama da ita sakamakon hare haren masu ikirarin jihadi, da suka haddasa mutuwar sama da mutane 2000 tare da tarwatsa sama da miliyan 1.5 daga gidajensa daga shekara ta 2015 zuwa yanzu.