A ranar lahadin data gabata ne iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwa, iyaye da ‘ya’yan su ne suka ziyarci jagoran harka islamiyya, sheikh Ibrahim Yaqoob Al-zakzaky a gidan sa dake Abuja.
A yayin ziyarar dai iyalan shahidai sunyi ganawa ta kai tsaye da jagoran tare da mai dakin sa malama zinatuddin, wacce take tare da shehin malamin tun lokacin da aka sake su bayan shafe kusan shekaru shidda a gidan yari.
Iyalan shahidan dai sun hada da, mai dakin shaheed muhammad mahmud Turi, mai dakin shaheed dakta mustapha, da kuma dan sheikh shahid kasim umar sokoto, iyalan malam Abukakar Jaji, da kuma mahaifiyar shahida batula muhammada gana, da dai sauran su.
A yayin ziyarar shehin malamin ya gaggaisa da iyalan shahidan kuma ya jajanta musu gami da basu hakuri bisa rashin ‘yan uwan su da sukayi, sa’annan ya gabatar da lambobin girmamawa inda ya mika su da kansa ga wakilan shahidan wadanda suka karba kuma suka nuna murna gami da farin cikin su.
Tun bayan fitowar shehin malamin dai wannan itace ganawa ta fili karo na uku da yake yi da ba’arin almajiran sa.
Da farko ya gana da mas’ulan harka islamiyya din kuma masu gudanar da gwagwarmayar nan shahararriya ta Abuja Struggle.
Bayan makonni kuma an gano shehin malamin yana ganawa da ‘yan uwan sa na jini wanda suka hada da yayan sa malam Abdulkadir yaqoob zakzaky wanda dan ahlussunnah ne.
Ganawa ta baya bayan nan itace wacce shehin malamin ya gana da ‘yan uwan shahidan kuma rahotanni sun tabbatar da cewa ganawar ta bada ma’ana kuma tayi wa ‘yan uwan shahidan dadi sosai.
Idan ba’a mance ba dai malam zakzaky ya shiga hannun jami’an tsaro ne tun a shekarar 2015 bayan da jami’an sojin najeriya karkashin jagorancin janar yusuf tukur buratai suka kai masa hari a gidan sa dake gyallesu, kuma tun wancan lokacin yake hannun jam’ian tsaro har zuwa shekarar 2021 inda babbar kotun gwamnatin tarayya kaduna ta wanke shi kuma ta sake shi tare da mai dakin sa.