Kungiyar da ke fafutukar ɓallewa daga Najeriya da son kafa Jamhuriyar Biafra wato IPOB, ta haramta yin taken Najeriya da cin naman shanu a wuraren bukukuwa da daukacin makarantun da ke Kudu maso gabashin kasar.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun kakakin ƙungiyar Chika Edoziem.
A cikin sanarwar, ƙungiyar ta fitar da sabbin dokoki bakwai da ta ce na sabuwar shekara ne da za ta fara amfani da su a 2022 ɗin.
Ga dai saƙon nata kamar yadda yake a sanarwar:
1. Saƙon farko ya ce a 2022 ƙungiyar za ta ci gaba da fafutukar ganin an saki jagoranta Nnamdi Kanu, wanda suka kira “fursunan da ake tsare da shi ba tare da ya yi laifi ba.” Ƙungiyar ta ce za ta kira fafutukar da taken “Kamfe don neman sakin fursunan da ake tsare da shi ba tare da ya yi laifi ba.”
A sakamakon wannan kamfe, ƙungiyar ta buƙaci dukkan mambobinta da al’ummar yankin da ta kira Biafra da su sauya hotunan da ke kan shafukansu na sada zumunta ta hanyar sanya fastar kamfe ɗin.
2. Saƙo na biyu shi ne wanda ƙungiyar ta umarci mambobin IPOB a ko ina a faɗin duniya da su gaya wa iyalansu wannan umarnin. “Za mu fara zanga-zanga a fadin duniya a manyan birane.
“Za mu yi zanga-zangar ce a ofisoshin jakadancin Birtaniya da Majalisar Dokokin Birtaniya da gidan Firaministan Birtaniya da ofisoshin jakadancin Kenya da na Najeriya da manyan ƙungiyoyin ƙasashen waje kamar su Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da Amnesty International da kuma kafafen yaɗa labarai,” a cewar sanarwar.Wa ye mutumin da ke fafutikar kafa kasar Biafra?
Abin da ya sa ƴan awaren Kamaru da na Najeriya suka haɗe kai
3. Abu na uku a jerin saƙonnin shi ne IPOB ta ce za ta ƙirƙiri wani sabon sashe da zai yi aiki a ƙarƙashin ƙungiyar. Ta ce za a ayyana sashen a matsayin Sashen Ilimi na IPOB.
“Babban aikin sashen shi ne koyar da tarihinmu da harshe da kuma al’adarmu ga ƴaƴanmu.
“Muna da littattafai uku da za mu wallafa a wannan shekarar nan don cimma hakan. Sannan bayan bayyana su ga al’umma, za a kira marubuta ‘ƴan yankin Biafra’ da kuma wallafa littattafai na ƴan firamare da sakandare.
Zebus cattle search for pasture on May 29, 2010.
4. Saƙo na hudu shi ne haramta yin taken Najeriya da ƙungiyar ta yi a kafatanin yankin Igbo daga sabuwar shekarar nan ta 2022 a dukkan makarantun yankin.
“Ƴaƴanmu ba za su ci gaba da yin abin da zai dinga tuna musu cewa suna ƙarƙashin danniya ba. Dole ne hukumomin makarantu su koya wa ƴaƴanmu taken namu yankin. Taken Ƙasar Biafra.”
5. Haramcin da ƙungiyar ta ce ta sanya wa ƴaƴanta a kan cin naman shanu zai fara aiki ne a watan Afrilun 2020.
“Daga wannan wata ba za a dinga amfani da shanun Fulani a kowace harka ko taro ba a ƙasar Biafra.
“A maimakon hakan za mu dinga amfani da shanunmu da muka kiwata ƴan asalin yankin a wuraren tarukan al’adunmu, kuma dole ne masu lura da garuruwa su tabbatar da wannan saƙon ya isa ga birane da karkara,” in ji sanarwar.
6. IPOB ta ce 30 ga watan Mayun 2022 zai zo da sabon salo. “Ita ce za ta zamo ranar da za mu yi bikin ƴancin kanmu.
“Za mu shirya taruka a manyan ɗakunan taro. Babu zanga-zanga. Kuma wadannan shirye-shiryen za a fara su ne ba tare da ɓata lokaci ba.”
7. A ƙarshe IPOB ta jaddada muhimmancin ɗa’a a kafatanin tsarinta. “Kowane ma’aikacin IPOB dole ya dinga kai kansa ga shugabansa.”
Sannan ta ja kunnen waɗanda suka kauce a baya da cewa har yanzu ƙofa a buɗe take ta karɓarsu idan suna son komawa “don kar su ƙwari kansu.”
Short presentational grey line
Tun a watan Oktoban 2021 ne kungiyar IPOB ta haramta wa Fulani Makiyaya shiga yankin da cin naman shanun da ake kai wa yankin daga arewacin Najeriya.
Amma a wancan lokacin ma kungiyar ta ce umurnin nata zai fara aiki ne bayan wata shida.
A bangare guda kuma, rahotanni daga jihohi biyar na shiyyar kudu maso gabashin Najeriyar na cewa al’ummomin yankin sun ci gaba da walwala da hada-hadarsu, sakamakon janye umurnin da kungiyar IPOB ɗin ta yi na hana fita ko tilasta wa jama’a zaman gida.
Ana hakan ne kuma rana ta ɓaci wa wani daga cikin kungiyar IPOB din, wadanda suka yi yunkurin kai hari da niyyar kona gidan wani basarake a jihar Imo, amma `yan sanda sun ce sun yi nasarar tarwatsa su, tare da kashe guda, yayin da ragiwar suka ranta a na kare!
Jagoran kungiyar IPOB din dai, wato Nnamdi Kanu yana hanu mahukunta a Najeriya, wanda ake masa shari’ar da ta shafi cin amanar kasa.
Sai dai ƴan kungiyar masu ra’ayin a waren sun ce za su bi hanyoyi daban-daban wajen matsa wa gwamnati lamba domin ta sake shi.