Kungiyar Kwallon Kafa ta Inter Milan ta doke abokiyar hamayyarta AC Milan da ci daya mai ban haushi da ya ba ta damar zuwa wasan karshe na gasar zakarun turai.
Tun da fari dai a satin da ya wuce Inter Milan ta doke AC Milan da ci 2 har gida, lamarin da ya sanya ta karkare wasanni biyu da kwallaye uku.
Inter Milan ta isa wasan karshe na gasar bayan shafe shekara 13 ba tare da ta sake zuwa wannan mataki ba.
Dan wasan gaban kungiyar Lautaro Martinez ya jefa kwallon daya da ta raba gardamar wasan.
A daren yau kuma za a fafata tsakanin Manchester City da Real Madrid da misalin karfe 8 na dare agogon Nijeriya.
Duk kungiyar da ta yi nasara za ta fafata wasan karshe da Inter Milan.
A wani labarin na daban mukaddashin mataimakin shugaban Jami’ar Koyarwa ta Modibbo Adama da ke Yola (MAU), Farfesa Muhammad Musa Malgwi, ya rasu a ranar Alhamis.
Sanarwar da Jami’ar ta fitar, mai dauke da sa hannun rajiistara, Hajiya Halima Bala, ta ce mamacin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, lokacin da yake gudanar da aikin da Jami’ar ta tura shi Abuja.
Ta ce mamacin wanda kafin rasuwarsa shi ne makaddashin mataimakin shugaban Jami’ar, ya rasu ya bar matarsa Farfesa Anna M. Malgwi, da ‘ya’ya.
Ta kara da cewa baya ga kasancewar Farfesa Malgwi, mukaddashin mataimakin shugaban Jami’ar ya kuma rike mukamai da dama a Jami’ar da kasancewarsa shugaban tsangayar kimiyyar zamantakewa.
Sanarwar ta ce nan gaba, iyalan mamacin za su sanar da lokacin jana’izarsa.