Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hare-haren da ake kai wa hukumar tare da ƙona mata dukiya a wasu jihohi abin damuwa ne, domin zai shafi ƙoƙarin da ta ke yi na inganta tsarin zaɓe a ƙasar nan.
Ya ce a cikin kimanin makwanni uku da su ka gabata, wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun ƙona ofisoshin INEC a ƙananan hukumomin Essien Udim da ke Jihar Akwa Ibom, da Ohafia a Jihar Abiya da Udenu da ke Jihar Inugu.
Ya ce a ranar 16 ga Mayu an ƙara saka wuta tare da yin ɓarna a ofishin jiha na INEC da ke Inugu inda aka lalata wasu sassa na ginin kuma aka ɓarnata ababen hawa, yayin da kuma akwai wasu muhimman kadarori waɗanda su aka fi maida hankali wajen kai wa hari.
Ya ƙara da cewa, “Ko a daren jiya Talata, 18 ga Mayu, an ƙone wasu ƙarin ofisoshi biyu ƙurmus a Ibonyi, waɗanda su ka haɗa da Ƙaramar Hukumar Ezza ta Arewa.
“Duk da yake ba a rasa rai ba, ɓarnar da aka yi wa ginin da kayan zaɓe ta wuce misali. Babu abin da ya tsira na daga akwatunan zaɓe da rumfunan katako na zaɓe zuwa injinan janareto, da kayan ofis da na aiki.
“Shakka babu, waɗannan hare-hare ba tsautsayi ba ne, sun fi kama da abubuwan da aka zauna aka tsara su musamman saboda INEC.
“A bayyane ya ke cewa waɗannan hare-hare ba su kamata ba kuma za su iya yin zagon ƙasa ga ƙudirin hukumar na shirya zaɓuɓɓuka kuma su illata tsarin yin zaɓe na ƙasar nan.
“Maye gurbin waɗannan kayayyakin a halin matsi da ake ciki yanzu ba ƙaramin aiki ba ne, don haka zai shafi ayyukan zaɓe a yankunan da abin ya shafa.
“Waɗannan kaya ba iyakar amfanin su wajen kaɗa ƙuri’a kaɗai ba ne, har ma ana amfani da su wajen wasu muhimman ayyuka na shirya zaɓe irin su rajistar masu zaɓe da tsara ayyukan masu ruwa da tsaki da aikin wayar da kan masu zaɓe.”
Yakubu ya ce babu shakka hukumar za ta haɗa gwiwa da hukumomin tsaro domin yaƙar ɓatagarin da ke aikata wannan ta’asa ta hanyar da doka ta tanadar, kuma a kan haka INEC za ta yi taro da dukkan hukumomin tsaro a ranar Litinin, 24 ga Mayu.
“An samar da waɗannan kayayyaki ne domin su amfani jama’ar yankin ta fuskar abin da ya fi komai tasiri a mulkin dimokiraɗiyya, wato zaɓe.
“Don haka lalata wannan muhimmin kadara ta ƙasa da ma’adanar kayan aikin zaɓe da aka ɗauki tsawon lokaci da kuɗi mai yawa don tanadar da su bai dace ba ko kaɗan.”
Yakubu ya yi kira ga kowa da kowa, musamman al’ummar da aka kai wa waɗannan kadarori na INEC, da su kalli kan su a matsayin mamallaka kuma masu tsare waɗannan kayayyakin kuma su taimaka wajen kare su.
Ya bayyana jin daɗi kan yadda har wasu garuruwan sun fara yin hakan, domin sun yi amanna kamar INEC da sadaukar da kai wajen inganta ayyukan shirya zaɓe a Nijeriya.
Ya ce, “A tsawon shekaru sun tallafa wa hukumar a wajen dukkan ayyukan shirya zaɓe daga Rajistar Masu Zaɓe zuwa aiwatar da zaɓen.
“Hasali ma dai wasu daga cikin su sun bada gudunmawar filayen da aka gina ofisoshin mu na ƙananan hukumomi.
“Ko a wannan ƙone-ƙonen da ɓarnar da aka yi, da yawan su sun nuna gagarumar amincewar su tallafa wa hukumar.
“Misali, bayan an lalata ofisoshin mu a Osun a lokacin zanga-zangar #EndSARS a cikin Oktoba 2020, al’ummar garin Ikirun da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ifelodun da wasu ƙauyuka biyu a Ƙaramar Hukumar Ede ta Kudu sun yi ƙoƙarin bada gudunmawa don a gyara ofisoshin, kuma su ka yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar wajen kare su a nan gaba.
“A Nnewi ta Arewa da ke Anambra ma, mutanen garin sun ce za su gyara mana ofishin mu na ƙaramar hukuma wanda aka lalata a lokacin zanga-zangar #EndSARS.
“Hukumar ba ta raina irin wannan haɗin gwiwar ba. Ina so in gode wa waɗannan al’ummomin da ke sassa daban-daban na ƙasar nan tare da yin kira a gare su da su ci gaba da kallon kayan INEC a matsayin na ƙasa baki ɗaya kuma nasu da ya dace su kare.”
Shugaban na INEC ya ce a halin da ake ciki yanzu, a taron da aka yi na kwamishinonin zaɓe ran Laraba an ɗauki bayanai daga gare su kan yadda ya kamata a yi domin kare kadarorin.
Yakubu ya bayyana cewa INEC za ta yi bincike mai zurfi domin ta yi amfani da daɗaɗɗiyar hulɗar da ke tsakanin ta da al’ummomin yankuna domin kare kadarorin ta, tare kuma da dogaro sosai da tallafin da hukumomin tsaro ke bayarwa.
Ya ce, “Daga nan kuma duk da barazanar da wannan ƙalubalen ke janyowa, mu na da yaƙinin cewa za mu samo ƙwaƙƙwaran maganin waɗannan hare-haren da ake kai wa kayayyakin mu.
“Amma tilas ne a gaggauta yin haka domin hana illata shirye-shiryen gudanar da zaɓuɓɓuka da ke tafe, musamman aikin Rajistar Masu Zaɓe wanda mu ka tsara aiwatarwa ba tare da yankewa ba a cibiyoyi 2,673 da ke faɗin ƙasar nan a tsawon sama da shekara ɗaya, kuma dubban jami’an INEC ne za su yi aikin tare da tallafin jami’an tsaro.”