Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta rantsar da Dakta Mahmuda Isah a matsayin Zaunannen Kwamishinan Zaɓe, wato ‘Resident Electoral Commissioner’ (REC) a karo na biyu.
A sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na shugaban hukumar, Mista Rotimi Oyekanmi, ya raba a Abuja, ya ce an rantsar da kwamishinan ne a ranar Talata a hedikwatar hukumar
Oyekanmi ya ce an gudanar da rantsarwar ne a wajen taron mako-mako na hukumar wanda Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, da kwamishinonin ƙasa da sakataren hukumar su ka halarta.
Ya ce a taron, Farfesa Yakubu ya shawarci Dakta Isah da ya ci gaba da sadaukarwa ga al’ummar Nijeriya sannan ya tabbatar a ko yaushe ya na bin hukunce-hukuncen da doka ta gindaya.
Shi dai Dakta Isah, an fara naɗa shi kwamishina ne a cikin Janairu 2018 kuma ya yi aiki a jihohin Jigawa da Kaduna kafin a yi masa canji zuwa Gundumar Babban Birnin Tarayya.
A wani labarin na daban shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana nadamar jagorantar taron da aka yi na tabbatar da Aminu Tambuwal a matsayin shugaban majalisar wakilai ta 7.
Aminu Tambuwal shine gwamnan jihar Sokoto mai barin gado kuma tsohon kakakin majalisar wakilai.
Da yake magana a Abuja a taron hadin guiwa – Majalisar 10 (Wakilai da Sanatoci), gamayyar mambobin jam’iyyar APC da jam’iyyun adawa a majalisar dokoki ta 10 mai zuwa a ranar Laraba, Gbajabiamila ya ce “na yi nadamar hakan,” – taimakawa Aminu waziri Tambuwal zama shugaban majalisar wakilai ta 7.
Gamayyar dai ta amince da ’yan takarar jam’iyyar APC a shugabancin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu, a majalisar wakilai ta 10.
Kafin Gbajabiamila ya yi magana, dan takarar shugaban majalisar dattawa na jam’iyyar APC, Sanata Godswill Akpabio, shi ma ya halarci taron inda ya yi wani takaitaccen jawabi sannan ya fice.