Bayan watanni uku da karewar wa’adin tsohon REC, hukumar INEC ta tura sabon kwamishinan zabe zuwa jihar Katsina.
Farfesa Yahaya Ibrahim Makarfi shine ya maye gurbin Jibrin Zarewa a matsayin sabon kwashinan zabe a jihar ta shugaban kasa Buhari.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmud yakubu ne ya rantsar da Makarfi a ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta nada Farfesa Yahaya Ibrahim Makarfi a matsayin sabon kwamishinan zabe (REC) na jihar Katsina.
Nadin na zuwa ne kimanin watanni uku bayan karewar wa’adin tsohon kwamishinan zabe na jihar, Jibrin Zarewa, jaridar Vanguard ta rahoto.
Shugaban sashin ilimantar da masu zabe da labarai, Mista Shehu Sa’idu shi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gudanarwa, wanda ke kula da harkokin hukumar tun bayan wucewar Zarewa a watan Agustan 2022.
Ya kuma yi aiki a matsayin lakcara a sashin tsara muhalli da awon gini.
Makarfi ya samu kyakkyawar tarba daga ma’aikatan INEC a Katsina Sabon kwamishinan zaben na jihar Katsina wanda ya kama aiki a ranar Litinin, 7 ga watan Nuwamban 2022 ya samu tarba daga sakataren gudanarwa, Isah Magaji Gummi da sauran ma’aikata a hedkwatar hukumar da ke jihar.
Daily Post ta rahoto cewa Farfesa Makarfi na cikin sabbin kwamishinonin zabe 19 da shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, Farfesa Mahmud yakubu ya rantsar a ranar 3 ga watan Nuwamban 2022.
Ya rantsar da su ne bayan sun tsallake tantancewar majalisar dattawa da samun yarda shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ana zaben kananan hukumomi a jihar Neja A yau Alhamis, 10 ga watan Nuwamba ne ake gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar Neja.
Domin baiwa al’ummar jihar damar sauke hakokinsu na yan kasa da kuma zabar yan takarar da suke so su wakilce su, gwamnatin jihar ta bayar da hutun kwana daya.
Da yake sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Minna, babban birnin jihar, babban sakataren gwamnatin jihar, Ahmad Matane ya ce shaguna da kasuwanni za su kasance a rufe a wannan rana.
SOURCE:LEGITHAUSA