Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta sanar da cewa, mutum sama da miliyan 93 ne suka yi rijistar zaben 2023 mai zuwa.
Kamar yadda hukumar ta bayyana a hedkwatarta da ke Abuja, ta sanar da cewa maza ne da kaso mafi yawa na masu rijistar zaben.
A cikin jihohin Najeriya kuma, jihar Legas ce ke kan gaba wurin yawan masu kada kuri’un inda jihar Kano ke biye da ita.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, tace ta yi wa masu kada kuri’a 93,469,008 rijista domin zaben 2023 mai gabatowa.
INEC ta Bayyana Adadin ‘Yan Najeriya da Suka yi Rijistar Zaben 2023.
Bayanin kan wadanda suka yi rijistar ya nuna maza ne suka kwashe 52.5% yayin da mata suka kwashi 47.5% na jimillar wadanda suka yi rijistar, jaridar The Nation ta rahoto.
Wannan na kunshe ne a jerin sunaye na karshe na wadanda suka yi rijista da hukumar zaben mai zaman kanta ta bai wa jam’iyyun siyasa a ranar Laraba a hedkwatarsu da ke Abuja.
Legas ce a kan gaba inda ta ke da mutum 7,060,195, sai Kano da ke biye da 5,921,370 na wadanda suka yi rijistar zaben. Karin bayani nan tafe…
A wani labarin na daban Sanata Ishaku Abbo mai wakiltan yankin Adamawa ta arewa a majalisar dokokin tarayya ya ce zai daukaka kara kan hukuncin kotu da ke haramta masa takara a zaben 2023 karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga hukuncin babban kotun jihar karkashin jagorancin Justis Danladi Mohammed wanda ya haramta masa takara a zabe mai zuwa.
Yayin da yake zartar da hukunci, Justis Mohammed ya riki cewa APC a karamar hukumar Mubi ya arewa ta kori Sanatan a ranar 7 ga watan Oktoba 2022, cewa bai da hurumin tsayawa takara a jam’iyyar. Kotu da ake ganin ita ce gatan talaka ta zama wajen ciniki, Abbo.
A wata hira da Channels TV, Abbo ya bayyana hukuncin kotun a matsayin wanda aka siye.
Ya koka cewa kotu da ake ganin ita ce gatan talaka ta zama na ciniki.
A cewarsa, hukuncin akwai tangarda saboda wadanda suka kore shi daga jam’iyyar ba jami’an karamar hukuma bane kuma saboda haka babu hujjar kore shi.
Bugu da kari, kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin APC, shugaban jam’iyyar na gudunma ne kadai yake da hurumin hukunta dan jam’iyya ba shugaban karamar hukuma ko na jaha ba.
Ya kara da cewar alkalin ya taba ba da umurni da ke hana shugabannin karamar hukumar daga daukar kansu a matsayin Jami’an jam’iyyar.
Abbo ya kuma tabbatarwa da Channels TV cewa zai daukaka kara a kotun daukaka kara sannan ya yi kira ga magoya bayansu da su kwantar da hankalinsu.
Bakano ya samu babban mukami a gwamnatin Kuros Riba A wani labari na daban, gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade ya yi garambawul a majalisarsa gabannin kammala wa’adin shugabancinsa.
Gwamnan ya nada sabbin kwamishinoni 12 ciki harda wani Bakano kuma musulmi na farko da ke samun irin wannan babban mukami a jihar.
Source:LegitHausa