Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana Malam Ibrahim Shekarau na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Kano ta Tsakiya.
Wannan rudani ya biyo bayan lashe zaben Sanata da Rufai Hanga na jam’iyyar NNPP da ya yi a ranar Asabar.
Amma tun kafin shiga zaben, Sanata Shekarau ya bayyana cewar tuni ya fice daga jam’iyyar NNPP kuma ba shi da wata alaka da jam’iyyar.
Kuma ya ce ya aike wa da INEC a rubuce cewar ya fice daga jam’iyyar amma ta sanar da shi cewar lokacin sauya sunan dan takara ya wuce.
Ita ma a nata bangaren, jam’iyyar NNPP ta ce ta sanar da INEC sauya sunan Shekarau da na Rufai Hanga biyo bayan ficewarsa daga jam’iyyar tare da komawa PDP.
Amma ana tunanin NNPP na iya garzayawa kotun kararrakin zabe don kalubalantar ayyana Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben.
A wani labarin na daban Muhammad Adamu Aliero ya kayar da Gwamnan Jihar Kebbi a takarar kujerar Sanatan Kebbi ta Tsakiya, inda ya samu kuri’u 126,588 yayin da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya samu kuri’u 92,389.
A lokacin da ya ke bayyana sakamakon zaben, Sanatan mazabar Kebbi ta Tsakiya, Farfesa Abbas Yusuf Bazata, ya ce “Sakamakon zaben kujerar Sanatan mazabar ta Kebbi ta Tsakiya da aka gudanar a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu ya bayyana kamar haka Sanata Muhammad Mainasara Adamu Aliero ya lashe zabe da kuri’u 126,588 da aka kada kuma suka lashe mafi yawan kuri’u, an bayyana su a matsayin wanda ya lashe zaben,” in ji shi.
Haka kuma Abubakar Atiku Bagudu ya samu kuri’u 92,389 a zaben da aka gudanar.
Ya bayyana cewa sauran ‘yan takarar jam’iyyun siyasa sun samu kuri’u daban-daban kamar yadda aka bayyana.
“Ya ce a matsayina na jami’in zabe da kuma karba da tattara sakamakon zaben kujerar Sanatan majalisar dattawa na Kebbi ta Tsakiya, kuma ikon da ya rataya a wuyana.
“Na ayyana Sanata Muhammad Mainasara Adamu Aliero na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben kuma ya samu mafi yawan kuri’un da aka kada kuma shi ne zababben Sanata na Mazabar Kebbi ta tsakiya a majalisar dattawa.