Indiya ta kori jami’in diflomasiyyar Canada
Indiya ta kori wani babban jami’in diflomasiyyar Canada.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar a birnin Delhi ta ce matakin da ta dauka na nuni da abin da ta kira kara nuna damuwa game da tsoma bakin jami’an diflomasiyyar Canada a cikin harkokin cikin gidan Indiya.
Sanarwar ta zo ne sa’o’i bayan ministan harkokin wajen Canada ya sanar da cewa an kori wani jami’in diflomasiyyar Indiya.
Rikicin diflomasiyyar da ke kara ta’azzara ya ta’allaka ne kan ikirarin Canada na cewa watakila jami’an gwamnatin Indiya na da hannu a kisan ɗan gwagwarmayar Sikh dan kasar Canada, Hardeep Singh Nijjar, a yankin British Columbia a watan Yunin wannan shekarar.
Sai dai Indiya ta kira wannan zargin a matsayin wauta.
Amurka ta nuna matukar damuwa a kan zargin da Canada ke yi wa Indiya kuma ta ce yana da matukar muhimmanci a gurfanar da wadanda suka aikata laifin gaban kotu.