IGP Alkali Usman Baba, Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya ya aminta da sauyawa kwamishinonin ‘yan sandan Najeriya 8 wurin aiki Kamar yadda rundunar ta bayyana.
An yi hakan ne domin karfafa aikin tare da tabbatar da shugabanci nagari a cikin aikin ‘yan sandan.
Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya musanta labaran da ake yadawa kan cewa an canzawa kwamishinan ‘yan sandan Kano wurin aiki kan rashawa.
Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, yayi umarnin sauyawa kwamishinonin ‘yan sanda takwas wurin aiki a jihohin kasar nan domin ingantuwar aiki da shugabanci.
Baba yace hakan zai inganta ayyukan ‘yan sanda a fadin kasar nan kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
Manyan jami’an ‘yan sanda da aka sauyawa wurin aiki sun hada da:
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe – Etim Effiom
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano – Maman Dauda
Kwamishinan ‘yan sandan Bauchi – Aminu Alhassan
Kwamishinan CPTU Staff College Jos – Babatunde Ishola
Kwamishinan X-SQUAD FCID Annex Legas – Mamman Sanda
Kwamishinan ‘yan sandan FCID Annex Gombe – John Babangida
Kwamishinan Safer Highway FHQ Abuja – Akinwale Adeniran
Kwamishinan DFA FCID Annex Legas – Abubaka Lawal
The Nation ta rahoto cewa, wannan na kunshe ne a wata takarda da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi ya fitar a ranar Alhamis.
Ba saboda rashawa aka sauyawa CP din Kano wurin aiki ba Adejobi ya musanta ikirarin da ake yi na cewa an sauyawa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano wurin aiki ne saboda zargin rashawa.
“Har ila yau, rundunar na son sanar da jama’a cewa da su yi watsi da labarin bogi da ake yadawa kan tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Abubakar Lawal, kan cewa an sauya masa jiha ne saboda zargin rashawa.
“Ana sake jaddada cewa sauya wurin aikin kwamishinonin rundunar abu ne da aka saba yi domin karfafa aikinsu tare da yada ilimi domin cigaban rundunar.”
– Yace. An aike sabbin kwamishinonin ‘yan sanda jihohi 4 a kwanakin baya.
A kwanakin bayan rundunar ‘yan sandan Najeriya ta aike sabbin Kwamishinonin ‘yan sanda jihohi hudu bayan na jihohin sun yi ritaya.
Daga ciki kuwa akwai jihohin Kano, Enugu da Zamfara.
A cikin wadanda wannan sauyin ya ritsa dasu a yanzu jihar Kano ce kadai.
SOURCE:LEGITHAUSA