Babban Sufeton ‘yan sanda (IGP), Alkali Baba, ya bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan za ta sa kafar wando daya da duk wanda ke ikirarin kasancewa dan kunfiyar IPOB ne.
Ya ce, ba zai yi wu a ce gwamnati na yaki da masu garkuwa da mutane ba da ‘yan fashi da kungiyoyin asiri a wasu sassan kasar nan sannan kuma wasu su bullo da wata fitina ta ikirarin kafa wata kasa.
Sabon shugaban rundunar ‘yan sandan ya yi wannan gargadin ne a shekaran jiya Juma’a, jim kadan bayan tabbatar masa da mukamin jagorantar rundunar ‘yan sanda.
“Mun fahimci akwai wata boyayyaiyar manfa wadda kungiyar a Kudu-maso-gabas dada Kudu-naso-kudu da kungiyar ke da ita. Haka kuma na yi Magana kan ta’addanci da kuma wasu nasu jakewa da addini su yi carna a Arewa-maso-gabas” in ji IGP.
“Za nu nemi hadin kan sauran jami’an tsaro domin kawar da dukkan ayyukan bata-gari a cikin fadin kasay nan da kuma tabbatar da al’umma na bin doka kamar yadda ya kamata”.
“Yanzu haka ana saun nasara wajen dakile aikata laifuka a Kudu-maso-gabas, saboda haka kawar da ayyukan bata-gari a wannan yanki sai mun yi hakuri, da haka za mu samu nasarar da muke bukata”.
“Da fara wannan yunkuri na samar da zaman lafiya a wannan yanki mun fara ganin ci gaba”.
“Abin daya kamata a kara fahimta shi ne, IPOB haramtacciyar kungita ce, saboda haka, ana haramtawa kowa shigarta”.
Sai dai abinda gwamnatin najeriya ta kasa ganewa shine, kungiyar IPOB tana goyon bayan manyan kasashen duniya kuma a shirye suke su goya mata baya a kan dukkan kudurorin da ta sanya a gaba.
Baya bayan nan duka a dalilin takaddama da kungiyar IPOB din gwamnatin najeriya ta shiga takun saka da kamfanin nan na tuwita inda har gwamnatin najeriyar tayi barazanar haramta amfani da manhajar tuwitar a fadin kasar.