Kwamitin agaji ta ‘Red Cross’ na kasa da kasa (ICRC) ya bayyana cewar kusan fararen hula 900 ne kawai ana gano a shekarar 2022 daga cikin mutum 15,000 da aka bada rahoton bacewarsu sakamakon aikace-aikacen ‘yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno da wasu sassan arewa maso gabas daga 2015 zuwa yanzu.
ICRC ta kara da cewa ta yi rijistan sama da mutum dubu 23,000 da suka bace a fadin Nijeriya sakamakon rikice-rikice.
Jagorar tawagar kariya da alaka da iyalai ta ICRC, Lillian Dube, ce ta shaida hakan a ranar Alhamis a bikin tunawa da mutanen da suka bace da ya gudana a Ngarannam, tsohowar sansanin ‘yan Boko Haram da ke Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.
“A shekarar 2022, ICRC ta samu nasarar gano mutum 900 da suka bace tare da maidasu ga iyalansu.
“ICRC na shirya taron tunawa da wadanda suka bace ne domin nuna goyon baya ga iyalan mutanen da suka bace. Mun yi rijistan mutanen da suka bace su 15,000 a jihar Borno da jihohin da suke arewa maso gabas.
Zai kuma iya kasancewa akwai wasu mutane da yawan gaske da su ma sun bace amma ba a samu shigar da su cikin rijista ba. Mutane da yawa a cikinsu an rabasu da iyalansu ne a 2015,” Dube ta shaida.
Shi kuma jami’in kiwon lafiyar kwakwalwa na ofishin ICRC a Maiduguri, Ahmed Kyari, ya ce, an ware ranar 30 ga watan Agustan 2023 domin tunawa da wadanda suka bace a rikice-rikice, ya kara da cewa, ta’addancin ‘yan Boko Haram ya shafi mutane da daman gaske a Borno.
Shi kuma a nasa jawabin, jagoran tawagar ICRC a Maiduguri, Mr Serge Zogg, ya mika sakon alhinunsu ga mutanen da aka raba da ‘yan uwa na tsawon lokaci.
Ta ce, ICRC ta kasance mai taimakon jama’a da agaji domin kare rayuka da mutuncin wadanda hare-hare ke shafa tare da sanar musu da tallafin da suke bukata.
Shettima Mohammed, wanda ya rasa ‘yar uwansa shekara 11 da suka wuce a rikicin Boko Haram, ya ce, har yanzu wannan rashin na sanya shi cikin dimuwa, ya ce, duk lokaci da aka bude kofar gidansa, gani yake kamar ‘yar uwansa ce ta dawo.
Ita ma Fatima Bunu Malik, da ta rasa kawunta a rikicin Boko Haram shekaru takwas da suka wuce a karamar hukumar Kukawa, ta misalta cewa matar kawun nata ta shiga matukar rashin hankali wacce ta rasu kwanakin baya, yanzu haka ‘ya’yansu guda uku duk sun zama marayu.
Source: LEADERSHIPHAUSA