ICC Tana Son Ganin An Kitse Batun Shari’ar Darfur Dake Gabanta.
Shugaban kotun kasa da kasa ta manyan laifuka Karim Khan wanda aka yi wa tambaya akan yiyuwar gurfanar da tsohon shugaban kasar Sudna Umar Hassan al-Bashir a gaban kuton da take a birnin Hague, ya bayyana cewa; Muna son ganin an kawo karshen shari’ar da ake yi danagne da yankin Darfur.
A jiya Talata ne aka gurfanar da tsohon kwamandan rudnunar Janjawid da ta jagorancin kisa, fyade da azabtar da mutanen Darfur na kasar Sudan, inda yaka fuskantar tuhume-tuhume har 31 masu alaka da laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.
Ali Muhammd Ali Abd-al-Rahman ya kasance na hannun damar shugaban kasar ta Sudan al-Bashir, shi ne kuma na farko da ya bayyana agaban kotun ta manya laifuka dake Hague, domin fuskantar shari’a akan batun na Darfur.
MDD ta bayyana cewa adadin mutanen da aka kashe a tsawon rikicin na Darfur ya kai 300,000, yayin da wasu miliyan biyu da rabi su ka bar gidajensu.
Shugaban kotun manyan laifukan ta kasa da kasa ya kuma cewa; Za a gabatar da dalilai akan yadda rundunar da Abd-Rahman ya jagoranta ta cutar da mutanen Darfur, da kuma jefa yara da mata cikin kangi da azaba.
A yayin da aka gabatar masa da tuhume-tuhumen da ake yi masa, Abd-Raham dan shekaru 72 ya kore cewa ya aikata wadannan laifukan, kuma shi ba shi da hannu a ciki.